Bincike kan ra´ayin wasu musulmi dangane da demoƙuraɗiyya da addini | Zamantakewa | DW | 08.02.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bincike kan ra´ayin wasu musulmi dangane da demoƙuraɗiyya da addini

´Yan ƙalilan ne daga cikin musulmin suke adawa da tsarin mulki irin na demoƙuraɗiyya

default

Musulmi suna salla a wani masallaci dake birnin Berlin

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Wani bincike da aka gudanar a nan Jamus an gano cewa saɓanin yadda da ɗaukacin ´yan ƙasar suke zaton cewa da yawa daga cikin musulmi na adawa da mulki irin na dimoƙuraɗiyya ba haka abin ya ke ba. Domin wasu tsiraru ne daga cikin masu bin dokokin addinin sau da ƙafa ke fatali da tsarin na dimoƙuradɗiyya. Kamar takwarorin su Jamusawa ko kuma waɗanda ba musulmi akwai wasu musulmin da ba sa bin dokokin addinin na su yadda ya kamata amma su ma suke fatali da tsarin na demoƙuraɗiyya. A kan haka ne Deutsche Welle ta tattauna da Farfesa Peter Wetzels na jami´ar birnin Hamburg wanda ya gudanar da wannan bincike domin jin ƙarin bayani musamman kan hanyoyin da suka bi wajen gudanar da binciken. Idan kun biyo mu a hankali muma za mu kawo cikakken bayani na sakamakon wannan bincike a shirin na yau.

Madalla.

To kamar yadda kuka ji a mabuɗin shirin a yau zamu yada zango ne a birnin Hamburg domin jin cikakken bayani dangane da wani bincike kan yadda wasu musulmi tsiraru a nan Jamus ke kallon tsarin demoƙuraɗiyya da kuma addini. Farfesa Peter Wetzels na cibiyar nazarin manyan laifuka a jami´ar birnin Hamburg shi ya jagoranci binciken da aka gudanar kan musulmi da yadda suke ɗaukar mulkin demoƙuraɗiyya da addini, yayi bayani dangane da sakamakon da suka cimma a wannan bincike yana mai cewa.

Wetzels:

“Wannan wani bincike ne da ya ƙunshi batutuwa da dama. Da farko mun fara jin ra´ayin musulmi ne mazauna wannan ƙasa. Mun faɗaɗa rukunin waɗanda muka yiwa tambayoyin inda muka shigar da matasa da ɗalibai kuma ´yan makaranta a ciki. Mun kuma gudanar da tattaunawa mai zurfi da musulmi dake cikin ƙungiyoyin masallatai da al´adu. Mun dai gano cewar musulmi da ake yiwa kallon masu tsattsauran ra´ayin addini su na nesanta kansu daga mulki na demoƙuraɗiyya to amma a hannun ɗaya su na neman ´yancinsu na tafiyar da addininsu a cikin ƙasa. Wannan rukuni na musulmi tsiraru ne a nan Jamus wato ba su fi kashi biyar cikin 100 na yawan musulmin da ke zaune a nan Jamus ba.”

Hakan dai na nufin kenan mafi rinjaye na musulmin a nan ƙasar ba su da irin wannan ra´ayi. To sai dai duk da haka akwai wasu musulmin waɗanda ba sa bin dokokin addininsu amma kuma suna fatali da wasu hukumomi na demoƙuraɗiyya. Suna kwatanta kansu a matsayin masu nesanta kansu da demoƙuraɗiyya daidai da wasu Jamusawa waɗanda ba musulmi ba ko kuma masu matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi da Yahudawa. Ganin cewa masu ƙyamar mulkin na demoƙuraɗiyya ba su da yawa ´yan tsiraru ne ko da akwai wani abin fargaba a dangane da wannan matsayin na su? Farfesa Wetzels ya yi bayani yana mai cewa.

Wetzels:

“Idan muka ba da la´akari da yawan musulmin dake nan Jamus da sauran mabiya addinai daban waɗanda a ra´ayinmu take-takensu ka iya zama wata barazana ga tsaron ƙasa, yawansu zai kai kashi 12 zuwa 14 cikin 100 na yawan al´umar musulmi dake nan ƙasar. Wato ko da yake ana yi musu kallon tsiraru amma ba za a iya yin watsi da su ba.”

A dai binciken jin ra´ayin dai an kuma mayar da hankali kan halayya ta musamman ga irin waɗannan tsirarun masu wannan ra´ayi na adawa da mulkin demoƙuraɗiyya. An dai gano cewar akwai wasu ƙananan ƙungiyoyi daban daban waɗanda daga cikinsu akwai baƙi da bisa rashin ƙwarewarsu a Jamusanci ba su saje da ´yan ƙasa ko kuma ba su da wata alaƙa ta ku zo ku gani da Jamusawa. Halayyarsu tana nuni da yadda suke da tsattsauran ra´ayin addininsu.

Wetzels:

“To sai dai a ɗaya ɓangaren akwai wani rukunin na mutanen waɗanda suka banbanta da na farkon musamman wajen iya yaren ƙasar. Su dai waɗannan mutanen masu ilimi ne da suke da hulɗa ta ƙut da ƙut da ´yan ƙasa kuma suke da damar tafiyar da ayyukansu cikin nasara a nan Jamus. A cikin wannan rukunin ma akwai waɗanda suke nesanta kanu da manufofi na demoƙuraɗiyya.”

Shin wani irin tasiri hakan ke yiwa ƙoƙarin inganta zamantakewa tsakanin Jamusawa da baƙi ´yan ƙaƙagida ko kuma akwai wata barazana da hakan ke yiwa tsaron ƙasar ta Jamus? Binciken dai bai ta´allaka kan ´yan tarzoma ko masu son tayar da zaune tsaye ba. Illa iyaka an mayar da hankali ne kan mutane masu ra´ayin ƙyamar mulkin na dokar ƙasa, inji Farfesa Wetzels. Ya ce muhimmin abu shi ne a gano dalilan da ke sa wasu bin ra´ayi na ƙyamar kundin tsarin ƙasar ta Jamus mai bin tafarki irin na demoƙuraɗiyya.

Wetzels:

“Mayar da wani rukuni na jama´a saniyar ware a cikin al´umma yana ɗaya daga cikin dalilan dake sa wasu ɗaukar wannan ra´ayi. Saboda shi yana da muhimmanci a haɗa kai da sauran ƙungiyoyin a tuntuɓar juna da ake yi tsakanin baƙi da mabiya addinai daban daban. Dole ne dukkan sassan da abin ya shafa su kawad da duk wani ra´ayi na son kai da nuna fifiko domin a samu kyakkyawan sakamako bisa manufar kyautata zamantakewa.”

Farfesa Wetzels ya kuma ba da shawarar yana mai cewa ya kamata a fito ƙarara a fayyace dukkan abubuwan dake hana ruwa gudu. Kamata ya yi a ƙara ɗaukar matakan wayarwa da matasa kai da yake a tsakaninsu ne aka fi samun yawan masu wannan ra´ayi na ƙyamar kundin tsarin mulkin ƙasa. Ga baƙi kuma dole ne a inganta hanyoyin tuntuɓar juna tsakanin hukumomi da ƙungiyoyin addinai da na al´adu dake cikin wannan ƙasa muddin ana son kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu a ƙokarin kyautata makomar al´umma da kaucewa shiga wani yanayi na ƙyamar al´adun juna.

 • Kwanan wata 08.02.2008
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/D4d9
 • Kwanan wata 08.02.2008
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/D4d9