1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan gangamin shugaban kasa a Habasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 25, 2018

Amirka ta tura jami'an leken asirinta na FBI zuwa Habasha domin su gudanar da bincike kan harin da aka kai wa sabon Firaministan kasar Abiy Ahmed a karshen mako

https://p.dw.com/p/30Gut
Äthiopien Kundgebung Premierminister Abiy Ahmed in Addis Ababa | Explosion
Harin ta'addanci a HabashaHoto: Oromo Media Network

An dai kai wannan harin ne yayin wani gangami na neman hadin kan al'ummar kasar Habasha wajen sauye-sauyen da Firaministan Abiy Ahmed ke yi a karshen mako. Kafar yada labaran gwamnatin Habashan ta EBC ta ruwaito cewa tuni jami'an suka isa Habashan, inda suke taimakawa wajen gudanar da binciken. Sama da mutane 150 ne suka jikkata yayin harin, inda kawo yanzu mutane biyu suka rasa rayukansu sakamakon raunukan da suka samu yayin harin. Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa yaga wani mutum sanye da kayan sarki na jami'an tsaro na kokarin harba gurneti, a gangami da aka gudanar mafi girma da kasar da ke zaman ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka.