Bill de Blasio ya kafa tarihi a birnin New York | Labarai | DW | 06.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bill de Blasio ya kafa tarihi a birnin New York

Ana samun sakamakon zabukan da aka gudanar a wasu jihohin kasar Amirka, inda zabukan ke nuna sabbin sauye-sauye.

Democratic mayor-elect of New York, Bill de Blasio, hugs his daughter Chiara and son Dante during his election victory party at the Park Slope Armory in New York, November 5, 2013. REUTERS/Carlo Allegri(UNITED STATES - Tags: POLITICS ELECTIONS)

Bill de Blasio da iyalinsa

Sakamakon zabukan da aka gudanar a wannan Talata a kasar Amirka, ya nuna Gwamnan Jihar New Jersey Chris Christie, mai sassaucin ra'ayi na jam'iyyar Republican ya samu gagarumar nasara inda ya doke Barbara Buono ta jam'iyyar Demokrat. Yayin da dan takarar jam'iyyar Demokrat Terry McAuliffe ya lashe zaben gwamnan Jihar Virginia, bayan da ya doke Ken Cuccinelli mai tsattsauran ra'ayi na jamiyyar Republican.

Sannan a karon farko cikin shekaru 20 dan jam'iyyar Demokrat ya lashe zaben zama magajin garin birnin New York, Bill de Blasio ya lashe zaben a birnin mafi girma da ke kasar ta Amirka. Zai karbi ragamar mulkin birnin daga hannun hamshakin mai arziki Michael Bloomberg, wanda ya mulki birnin na tsawon shekaru 12, inda ya yi wa'adi uku a jere.

Mawalfi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman