Bikin zagayowar cikkar shekaru 48 da kafuwar Fatah | Labarai | DW | 04.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin zagayowar cikkar shekaru 48 da kafuwar Fatah

Duban jama'a magoya bayan ƙungiyar Fatah mai fafatukar samar da yancin Falasɗinu ta gudanar da shagulgulan a yankin da ke ƙarƙashin iko kungiyar Hamas

Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar Hamas ta ba da izini ga kungiyar Fatah domin gudanar da bukukuwan kafuwar kungiya a yankin Gaza da ke a karƙashibn ikon ƙungiyar ta Hamas

masu aiko da rahotanin sun ce jama'ar mata da maza da kuma yara sun yi ta raira waƙoƙin tare da ɗaga tutar Fatah da ta Falaɗinu.Kasim na daya daga cikin waɗanda suka halarci gangamin.Ya ce ''na zo ne nan saboda gangamin da aka shirya

Masu lura da al amuran yau da gobe na furcin cewar wannan wata alama ta ƙara samun haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin biyu waɗanda suka daɗe suna gaba da juna.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu