Bikin tunawa da hatsarin tashar nukiliya ta Fukushima a Japan | Labarai | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin tunawa da hatsarin tashar nukiliya ta Fukushima a Japan

Mutane dubu 16 suka mutu a cikin hatsarin tashar nukliyar, yayin da wasu sama da dubu biyu suka yi ɓatan dabo, kana wasu dubu 160 suka tsere daga gidajensu.

Hukumomi da al'umma a ƙasar Japan sun yi tsit na wasu 'yan mintoci, domin tunawa da hatsarin nukiliyar na tashar Fukushima da aka samu, a sakamakon girgizar ƙasar da ta haddasa igiyar ruwa ta tsunami, da suka afkawa yankin arewa maso gabashi na ƙasar a cikin watan Maris na shekara ta 2011.

An gudanar da bukukuwa na tunawa da hatsarin a garuruwan Tokyo da kuma inda lamarin ya auku, tare da halarta shugabanni da kuma sarakunan gargajiya.. Dubun dubatar masu zanga zangar ƙin jinin nukiliya sun gudanar da wani gangami a cikin ƙasashe daban daban na duniya. A yanzu dai tashoshin nukiliyar guda biyu ne suke aiki, bayan an rufe sauran tashoshin sakamakon girgizar kasar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal