Bikin shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Chaina | Siyasa | DW | 01.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Chaina

An yi gagarumin bikin cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Mutanen Chaina karkashin tsarin jam'iyyar Kwaminisanci, inda Chainar ta gabatar da sabbin makaman yaki na zamani da ta kera

Lokacin wannan biki wanda aka yada a akwatinan talabijin, kasar ta Chaina ta nuna irin karfi da take da shi a bangaren tsaro. Shugaba Xi Jinping gami da sauran jiga-jigan gwamnati suka halarci gagarumin bikin. Kimanin dakaru dubu 15 suka shiga faretin na shekara-shekara da ke nuna irin karfin da kasar take da shi. A wannan karon an nuna sabbin kayan yaki da kasar ta kera. Wani dan shekaru 70 da haihuwa mai suna Yan Baotian wanda ya yi ritaya daga aiki ga abin da yake cewa:

"Na ji dadi! Daga shugabancin Shugaba Mao inda aka fara sabuwar Chaina ake ginawa har yanzu shekaru 70 da suka gabata. Daga kasa mai cike da tsananin talauci da ke baya tsakanin kasashen duniya zuwa kasa mai arziki haka ake yanzu. Chaina kamar yadda ake gani za ta shiga cikin kasashe masu karfi da arziki. Karfi soja da tattalin arziki tana gaba a duniya. A matsayi na wanda nake shekaru daya da wannan jamhuriya, ina cike da alfahari."

 

Kimanin mazauna birnin Beijing dubu 30 aka zaba domin zuwa dandalin faretin. Yara kanana 'yan makaranta suna cikin wadanda suka halarci bikin tare da iyayensu. Zhang Huaiqiu dan shekaru 12 tare da mahaifiyansa ga abin da yake ji kan wannan biki:

"Ina murna. na ga karfi sojoji da Chaina take da shi. Haka ya kara bude mun fahimta da nake da ita."

 

Wannan dandali na birnin Beijing fadar gwamnatin Chaina na cike da mutane daga bangarorin rayuwa dabam-dabam. Matashi Chen Yang ya ce dandazon mutanen da suka halarci bikin ya birge shi:

"Mutane masu yawan gaske sun fito. Kowa na murna. Kowa na da fata na gari kan kasarmu za ta karfafa ta kara karfi. Karfin shi ne samar mana da zaman lafiya."

 

Liu Shuxian dan shekaru 63 da haihuwa mai kula da dakin karatu a jami'ar birnin Beijing ya yi karin haske kan sauyi da aka samu a Chaina cikin tsawon rayuwarsa:

"Ina tsammani mutanen Chaina sun saba rayuwa karkashin sarakuna cikin shekaru dubu biyu akwai tunanin duk abin da aka tsayar shi ke nan. Akwai nasarori da haka ya kawo, kamar a wuraren aiki duk abin da shugaba ya ce shi ke nan. Haka kan saka shugaba jin dadi. Amma wannan rashin sanin ya kamata ne. Akwai lokacin da ya dace mutane su yi tunani wa kansu. Ya kamata mu ji daga wani bangaren."

 

An yi bikin na Chaina lokacin da masu zanga-zanga a yankin Hong Kong ke neman ganin an kara karfafa dimukuradiyya a yankin. Sai dai Shugaba Xi Jinping na Chaina ya yi alkawarin kasar za ta ci gaba da mutunta tsarin kasa daya hanyoyin mulki dabam-dabam.))