Bikin sallah na hada kan Musulmi da Kirista a Najeriya | Siyasa | DW | 12.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin sallah na hada kan Musulmi da Kirista a Najeriya

Limaman coci-coci da sauran Kiristoci a Najeriya na shagulgulan bikin sallah tare da Musulmai domin kara karfafa dangantaka tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Nigeria Ramadan

Hawan sallah na zama cikin manyan abubuwa da ke kawata bukukuwan na sallah

Yayin da Musulman duniya ke shagulgulan bikin babbar sallah a ranar Litinin din nan, limaman coci-coci da sauran manyan malaman addinin Kirista a Najeriya na taya daukacin Musulmin duniya barka da sallah tare kuma da yin kira wajan tabbatar da ganin ma su shagulgulan sallar sun taimaka wa 'yan gudun hijira da nakasassu da almajirai da mazauna kurkuku da abinci don su ma su san cewa ana bikin sallah.

Pastor Yohanna Buru da ke zaman shugaban wani babban coci a Sabon Tasha

Eid Al Fitr in Zinder, Niger

Bikin sallah ya zo a matsi na tattalin arziki

Kaduna ya bayyana ce: "Muna taya daukacin Musulmin duniya murna da zuwan wannan lokaci, kuma muna matukar fatan Allah Ya sa a kammala wannan shagulgula cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma muna janyo hankalin Musulmai da sauran alumma kasar a kan mahinmancin taimaka wa marasa karfi a wannan lokaci bisa la'akari da ganin irin matsalolin da talakawan kasa suka fada na matsin tattalin arzikin kasa".

Auf der Flucht vor Boko Haram Pastor Yohanna Buru

Pastor Yohanna Buru mai fafutikar hada kai tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya

Shi kuwa Evangelist Jonathan cewa ya yi wannan lokacin murna ne ga baki daya, kuma dole ne su ziyarci Musulmai domin lokacin Kirsimeti Musulmai sun ziyarce su.

Alaramma Abdulrahman Mohammad Bichi ya ce wannan shi ne zumunci, wannan abin ban sha'awa ne kuma su na yin kira ga sauran attajiran Najeriya wajen tabbatar da ganin cewa sun rika taimaka wa alumma domin kawo hadin kai da cigaba.

Sauti da bidiyo akan labarin