1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bikin Maulidi ya gudana lami lafiya a Kaulaq

October 19, 2021

An gudanar da sallar Maulidi ta bana a birnin Kaulaq da ke kasar Senegal lafiya lau tare da bin dokokin kaucewa kamuwa da cutar COVID-19.

https://p.dw.com/p/41sMs
Senegal | Maulid Festival
Hoto: Al-Amin Suleiman Muhammad/DW

Hukumomi a kasar Senegal sun sassauta dokoki da ka'idodji na cutar COVID-19 abin da ya baiwa dubun dubatar mutane daga sassan duniya shiga kasar domin halartar Sallar Maulidin wannan shekara.

Maulidin na bana na Madina Kaulaq ya samu halartar al'ummar musulmi daga kusan dukkanin sassan duniya, inda baya ga wadanda suka shiga kasar ta jiragen sama da na ruwa akwai al'ummar musulmi musamman daga sassan nahiyar Afirka da suka shiga kasar ta mota abin da ba a samu yin haka a shekarun bayan nan ba.

Mata ba a barsu a baya ba wajen halartar bikin Maulidin a garin Kaulaq
Mata ba a barsu a baya ba wajen halartar bikin Maulidin a garin KaulaqHoto: Al-Amin Suleiman Muhammad/DW

A sakon sa na alamta wannan rana mai matukar muhimmanci ga al'ummar Musulmi wato ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, babban Khalifan Darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Mahi Sheikh Ibrahim Niass ya ja hankulan hukumomi na duniya da su dakatar da zubar da jinin da ake samu a wasu sassan duniya.

"Ya ku bakin Manzon Allah (SAW) masoyansa masu yi masa hidima daga ko ina cikin duniya, muna godiya ga Allah (SWT) da sa mu a cikin masu yin wannan Sallah ta murnar haihuwar fiyayyen Annabi (SAW) don girmama shi. Muna karanto tarihinsa wanda ke zama abin koyi gare mu. Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya mafificin halitta. Saboda mun yi imani Allah bai girmama wata halitta sama da Annabi Muhammadu (SAW) ba."

A karon farko tun bayan nada shi Khalifan Tijjani na Najeriya Sarkin Kano na 14 Sheikh Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi ya samu halartar wannan Maulidi.

Sheikh Abdulwadud Harun wanda ya samu halartar wannan taron Maulidi daga Kumasi kasar Ghana ya ce ya godewa Allah da Ya nuna masa wannan rana.

Garin Kaulaq ya ga dandazon al'ummar Musulmi kamar nan a Maulidin 2020
Garin Kaulaq ya ga dandazon al'ummar Musulmi kamar nan a Maulidin 2020Hoto: Al-Amin Suleiman Muhammad/DW

Mustapha Sale Adhama daga gidan Wazifa Kano ya kwashe shekaru ya na zuwa wannan Maulidi amma ya ce bai taba ganin irin taron bana ba.

Yayin da ake fargabar kamuwa da cutar COVID-19 saboda dandazon jama'a, Sheikh Salahudeen Niass daya daga ciki shugabannin shirya wannan taro ya ce an dauki matakai na kare al'umma.

An yi karance-karance na tarihin Annabi (SAW) da ke nuna yadda ya kamata al'umma su kwaikwayi halayensa da kuma wakokin yabonsa kamar yadda aka saba a wannan taron Maulidi.