1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Bikin maido da kayayyakin tarihi

Ramatu Garba Baba
November 20, 2021

Rikicin Habasha bai hana gwamnatin kasar gudanar da bikin karbar kayayyakin tarihinta da Britaniya ta sace sama da shekaru 150 da suka gabata ba.

https://p.dw.com/p/43HtB
Precious artefacts looted by British soldiers returned to Ethiopia
Hoto: Solomon Muchie/DW

 

A wannan Asabar aka baje kayayyakin a kofar wani ginin ajiyan kayayyakin tarihin kasar don kowa ya gani. Jakadan kasar a Britaniya Teferi Melesse, da aka mika wa kayayyakin a hukumance watanni biyu da suka gabata a Britaniyan kafin ya kai su Addis Ababa, ya baiyana farin cikinsa inda ya baiyana nasarar maido da kayayyakin a matsayin gagarumin ci gaba mai matukar tasiri.

Habasha ta bi sahun sauran kasashen Afirka, da ke ci gaba da yin kira ga kasashen da suka sace kayayyakin tarihinsu a lokacin mulkin mallaka da su gaggauta maido su a maimakon adon da suke yi da su a dakunan tarihinsu a kasashen nahiyar Turai.