1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Mabiya addinin Kirista na ci gaba da bikin Kirsimeti

December 26, 2023

shakeru biyun da suka gabata an yi bukukuwan Kirsimeti a wani yanayi na daban sakamakon yadda duniya ta rude bayan annobar covid, masassarar tattalin arziki da wasu dalilai makamanta. Yaya al'amarin yake a bana?

https://p.dw.com/p/4aanw
Bikin Kirsimeti
Bikin KirsimetiHoto: Xabiso Mkhabela/AA/picture alliance

 

A Ghana muhimmun abubuwan da ke jan tafiyar a lokacin bukukuwan Kirsimeti shi ne nuna godiyan zagayowan shekara da al'uman Kirista ke yi wanda ke kuma shaida ziyarce-ziyarcen 'yan uwa da wuraren bude ido da shakatawa. Sai dai sutura da abinci na kan gaba. Duba da yanayin matsin rayuwa da karancin kudi shagon shinkafa da man girki wanda su ne kan gaba a cikin lissafin bukukuwan. To sai dai ta fannin mabiya addinin Kirista wadanda ke mayar da hankali kan ibada inda suke mayar da hankali a coci, da kuma wadanda a gare su lokaci ne na cin duniyarsu da tsinke.

Karin Bayani: Shirin bikin Kirsimeti a Najeriya da Nijar

Bikin Kirsimeti
Bikin KirsimetiHoto: AP

A jihar Lagod da ke Najeriya, Mr Samuel Ade mazauni a lardin Obalande ya ce lokaci ne  a yau na zuwa wuraren bude ido da sada zumunta domin sabunta zumunci ga 'yan uwa da abokan arziki ciki kuwa har da mabiya sauran addinai. Ko shakka babu duk da cewa ana cikin matsin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu Madam Joy wacce ta shigo Lagos daga Abuja ta bayyana cewa baki ne daga ake gudanarwa cikin nishadi da walwala gami da kai yara wuraren wasa.

To sai dai a cewar Pastor Bitrus wannan lokacin  bikin na Kirsimeti ya zo lokacin da ake fuskantar matsalar rashin abun hannu ga 'yan kasa inda hauhawar farashin kayayyaki suke neman gagarar talakawa.