Bikin kama aiki na shugaban Mali | Labarai | DW | 19.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin kama aiki na shugaban Mali

Tun 4 ga watan Satumba ne Ibrahima Boubakcar Keita ya yi rantsuwar kama aiki. Amma sai a yau alhamis ya ke gudanar da bikin da Shugabanni da dama suka halarta.

shugabannin kasashe duniya ciki har da na Faransa Francois Holland sun hallara a birnin Bamako domin shaidar da bikin kama aiki na sabon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita. Ana sa ran sabon shugaban zai yi jawabi inda zai bayyana manufofin gwamnatinsa.Tun a ranar 4 ga watan Satumba da muke ciki ne dai Keita da aka zaba a ranar 11 ga watan Agusta ya yi rantsuwar kama aiki ba tare da gudanar da biki ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin ta Mali ta tsayar da 24 ga watan Nowamba mai zuwa a matsayin jadawalin zagayen farko na zabe 'yan majalisa, yayin da zagaye na biyu kuma zai gudana a ranar 15 ga watan Disemba.

Shugabannin da ke halartar bikin ciki har da na Chadi Idris Deby Itno da kuma na Gabon Alin Bongo Ondimba za su yi amfani da wannan dama wajen gudanar da wani kwarya-kwaryar taron koli domin yin nazarin hali da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke fama da riginginmu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu