Bikin gargajiya na zane-zane na Chale Wote a birnin Accra, Ghana
Bikin gargajiya na Mantse Agbonaa karo shida da aka saba gudanarwa a kan tituna, ya samu halartar kwararru a fannin zane-zane sama da 200. Bikin na mako guda, ya gudana ne a unguwar Jamestown da dumbin 'yan kallo.
Zane-zane da rayuwa
Bukin na wannan shekara ya mayar da hankali ne kan manufar mahalarta wajen kirkirar wasu zane-zane da ke zama wani sabon abu ga rayuwar Dan Adam, wanda ya saba wa wanda aka saba gani.
Zane-zane tamkar a gaske
Wasu masu zane-zane sun zana tare da fenta wani hoto tamkar na gaske a gaban dumbin 'yan kallo suna shewa. A ranar 15 ga watan Augusta ne aka fara bikin gargajiyan da baje kolin zane-zane, wanda ke bayyana irin basirar zane-zane da ake da su a Ghana.
Zane-zanen kan titi
A karon farko titunan birnin Accra sun haskaka da zanen Kingsley Deffor. Abun da ya dauki hankali a bikin na wannan karon shi ne yadda kwararru a wannan fanni suka yi ta fenta titunan Accra, hade da mawaka da makada domin nishadantar da 'yan kallo.
Rawa da kade-kade
Zane-zane na tafiya ne kafada da kafada da nishadantarwa. A kan haka ne ma mawaka da makada suka yi ta cashewa a wurin bikin gargajiyar.
Lauye-lauyen jiki
Basirar lankwasa jiki ta hanyoyi dabam-dabam sun kasance abun sha'awa ga masu zane-zane da 'yan kallo da suka halarci bikin na Accra.
Launukan gaskiya
Tsawon mako guda da aka dauka ana gudanar da wannan biki dai, launukan tutar kasar Ghana watau Ja da Ruwan Kwai da Kore, su suka mamaye ko ina.
Tsohon garin Jamestown
A bayyane take dai cewar wannan bangaren birnin Accra da ake kira Jamestown, tsohon gari ne da ke da muhimmanci a tarihin birnin.
Fada mai ma'ana
Yara na bangaren mafi yawan mahalarta wannan biki. A nan ana iya ganin yadda wasu yara biyu suka shiga bikin danbe.
Mene ne hoto?
Ba a bukatar hoton wani abu da za a zana a inda ake da titi mai tsawo domin yin zane-zane da fenti.
Tsoffi da Sabbi
Dukkan abubuwan da aka gabatar a wurin bikin ya saba wa al'adun kasar Ghana da kewaye da aka saba gani.