Bikin cikar shekaru biyu da yin juyin juya hali a Masar | Labarai | DW | 25.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin cikar shekaru biyu da yin juyin juya hali a Masar

Yan adawa na shirin gudanar da wani gangami dangane zagayowar cikkar shekaru biyu da yin juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin shugaba Hosni Moubarak

Ƙungiyar jam'iyyun hammayar ta yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da zangar cikin lumana ta ƙin jinin gwamnatin Mohammed Morsi da kuma jam'iyyar sa ta yan uwa musulmi;saboda tsare tsare na siyasa da gwamnatin ta amince da su.Sai dai a jajibirin taron wasu ɗaruruwan jama'ar da suka gudanar da zanga zanga a dandalin Tahriri sun yi taho mu gama da yan sanda a sa'ilin da suke ƙoƙarin cire shingaye da aka dasa a filin da ke gewaye da manyan gine gine gwamnatin.

Shugaba Mohamed Morsi a cikin wani jawabin da ya yi ta gidan telbijan da rediyio na ƙasar ya gargaɗi jama'a.Ya ce'' ina yin kira ga ɗaukacin al'ummar ƙasar masar da su gudanar da wannan biki cikin lumana da kwanciyar hankali cikin yanayi na mutunta dokokin ƙasa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu