Bikin baje kolin zane-zane a Ghana
Daruruwan mutane da suka kware wajen zane-zane da zayanna ne daga Ghana da Lesotho da Kenya da Najeriya suka hadu a birnin Accra na kasar Ghana don yin bikin baje kolin zane-zane ta Chale Wote.
Baje kolin zane-zane
Masu zane-zane da dama sun baje kolin irin fasahar da suke da ita a bikin baje kolin zane-zane na Chale Wote karo na 7 da ya gudana a birnin Accra na Ghana. An gayyaci 'yan kallo da dama don su nuna irin tasu fasahar ta zane-zane.
Amfanin da ruwa ke da shi ga rayuwa da zane-zane
Kungiyoyi sun yi shiga irin ta gargajiya inda wasu kamar wadannan mutanen 'yan garin James Town da suka sanya fararen kaya. Mutanen sun yi amfani da ruwa domin nunawa duniya irin muhimmanci 'yancin fadin albarkacin baki da kuma bada dama ta bayyana abinda mutum ya yi niyya.
Yara ma sun samu damar nuna fasaharsu
Kananan yara ma sun shiga an dama da su a bikin nuna fasaha na Chale Wote. Wadannan yaran da suka shafe jikinsu da fenti sun yi ta zane-zane a gefen titi inda iyayensu ke kallonsu kana suke basu kwarin gwiwa.
Amfani da gawayi wajen yin zane-zane
Wannan matashin na nuna baiwar da ya ke da ita wajen zana mutane ta hanyar amfani da gawayi. Mutane da dama sun yaba da irin kokarin matashin.
Amfani da keke wajen nuna bajinta
Baya ga baje kolin zane-zane da a ka yi, mutane irinsu Martin Kwaku Abrokwah na kungiyar "Flat Land Boys" sun nuna irin kwarewarsu wajen sarrafa keke.
Al'adar al'ummar Ga
Baya ga zane-zane da kade-kade da raya-raye, bikin baje koli na Chale Wote kan bada dama ga mutane su nuna irin al'adunsu na gargajiya. Wadannan mutanen da suka fita daga Jamestown na kokari ne na nuna irin al'adar al'umma ta kabilar Ga da ke kasar Ghana.