1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Berlinale: Fina-finan Afirka kan sabon salo na hijira

Elizabeth Grenier, SB/AH
February 16, 2022

Fim din Najeriya da wani sabon shiga daga Sudan ta Kudu sun sake duba yadda Afirka ke kallon batun hijira a bikin baje kolin fina-finai na birnin Berlin da ake wa kira Berlinale.

https://p.dw.com/p/473eX
 Hoto daga fim din "No U Turn" na Ike Nnaebue
Dan Najeriya mai shirya fina-finai Ike Nnaebue da ya yi fim din 'No U-Turn,' ya yi tafiye-tafiye da bas a AfirkaHoto: Jide Akinleminu

Fina-finan Najeriya sun kasance cikin tsarin wadanda ake bajewa a bikin baje fina-finai na birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, sai dai a wannan shekara kasar Sudan ta Kudu ta samu shiga a karon farko kan batun hijira daga Afirka. A bana daga Najeriya akwai Ike Nnaebue wanda yake da sha'awar labarai irin na tatsuniya tun yana yaro saboda yadda kakarsa ta saba ba shi labari, kuma daga bisani ya zama mai shirya fina-finai.

Amma kafin fara wannan harkar ya duba irin yadda 'yan Afirka ke kokarin ketare tekun Bahar Rum domin samun rayuwa mai inganci a kasashen Turai: "Ina matukar son fadin labari tun ina yaro karami. A gaskiya yana cikin abin da zan iya tunawa a rayuwata. Ina son ra'ayin fadin labari."

Bayan ya duba rayuwar 'yan Najeriya da ke zuwa arewacin Afirka domin shiga Turai, ya rubuta labarin fim mai take "No U-Turn" wato "Babu komawa da baya" wanda aka zaba a bikin baje finai-finai na birnin Berlin, wato Berlinale.

Mai shirya fim Ike Nnaebue
Ana yi wa Ike Nnaebue kallon daya daga cikin sabbin fitattun masu shirya fina-finai a AfirkaHoto: Jide Akinleminu

Ya yi wannan tafiyar a shekarar 1995 lokacin yana dan shekaru 20 da haihuwa. Kuma wannan labari yana cikin guda biyu na Afirka da aka zaba a bikin na bana.

Fim na biyu shi ne mai taken "No Simple Way Home" wato "Babu saukin zuwa gida" da Akoul de Mabior ta rubuta da ke zama na farko daga Sudan ta Kudu a bikin na birnin Berlin. Ita dai Akuol de Mabior 'ya ce ga Marigayi John Garang de Mabior, wanda jagoranci gwagwarmayar Sudan ta Kudu gabanin ta samu 'yanci a shekara ta 2011. John Garang ya rasu makonni uku bayan nada shi makamin mataimakin shugaban kasar Sudan na farko a shekara ta 2005. A shekara ta 2013 sabuwar kasar Sudan ta Kudu ta tsunduma cikin yakin basasa.

'Yan Afirka da ke halartar bikin baje kolin fina-finan

Mai shirya fim Akuol de Mabior
Akuol de Mabior mai shirya fina-finai 'yar kasar Sudan ta KuduHoto: Akuol de Mabio

A shekara ta 2020 an nada mafiyar marubuciyar fin din Rebecca Nyandeng de Mabior daya daga cikin mataimakan shugaban kasa guda biyar bisa gwamnatin hadin kan kasa. Ga abin da Akuol de Mabior marubuciyar ke cewa:

"Kasancewa yaran 'yan gwagwarmaya haka ya kirkiri wani kishi da muke da shi. Duk da cewa ba mu taba rayuwa a kasar Sudan ta Kudu, muna jin irin cewa kar mu saki jiki a Kenya saboda wata rana za mu koma Sudan ta Kudu."

Bunkasar kasuwancin harkokin fina-finai ta intanet sakamakon corona

Bayan da duniya ta fuskanci annobar cutar coronavirus al'amura sun yi tsaye, amma an samu bunkasa ta hanyoyin kasuwanci da sauran harkokin rayuwa ta intanet, kuma a cewar Ike Nnaebue haka ya bunkasa fina-finan 'yan Afirka, musamman wadanda suka samu shiga kafar Netflix da wadanda ake sayarwa ta kafar Amazon da suka hada da litattafai:

"Wannan shi ya saka Netflix yake samun tasirin kasuwanci a nahiyar Afirka yanzu, ga Amazon shi ma ya kaddamar da shiri a Najeriya. Domin haka ya taimaka ga masana'antar hada fina-finai, saboda a tsohon tsarin ana sayar da faifan CD wadda ke cike da matsalolin masu satar fasaha da suke samun komai."