1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden zai nemi wa'adi na biyu

Usman Shehu Usman
April 25, 2023

Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya sanar da anniyarsa ta tsayawa takarar wa'adi na biyu a zaben kasar badi inda ya kawo karshen rade-radin da ake yi kan batun takarar

https://p.dw.com/p/4QXZd
Irland, Ballina, | US Präsident Joe Biden
Hoto: Leon Neal/Getty Images

Joe Biden wanda ya sanar da haka bayan an yi ta rade-radin cewa ba zai nemi wa'adi na biyu kasancewa tuni shekarunsa suka ja. Domin izuwa badi lokacin da za a gudanar da zaben Amirka, shugaban na Amirka zai cika shekaru 81 da haifuwa, yayinda kuma in har ya yi nasarar lashe zaben a badi, to kafin ya kammala wa'adinsa na biyu zai cika shekaru 86 a duniya. A 'yan watannin nan dai, farinjinin Biden ya yi matukar faduwa a tsakanin Amirkawa bisa dalilai masu yawa da suka shafi siyasar Amirka na ciki da wajen kasar. Shi ma dai mutumin da Joe Biden ya kayar a zaben da ya gabata Donald Trump, ana saran zai nemi yin takara in har jam'iyarsa ta amince da bashi tikiti.