1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwa na cikin garari saboda sauyin yanayi

Abdullahi Tanko Bala
November 11, 2022

Shugaba Amirka Joe Biden ya nanata cewa kasarsa za ta cimma kudirinta na rage hayakin masana'antu nan da shekarar 2030

https://p.dw.com/p/4JPjS
Ägypten | COP27 Klimakonferenz in Scharm El-Scheich | Joe Biden
Hoto: Saul Loeb/AFP

Shugaban Amirka Joe Biden ya nemi afuwa dangane da janyewar da Amirka ta yi daga yarjejeniyar sauyin muhalli ta duniya a birnin Paris yana mai cewa kasarsa ta na kokarin tunkarar matsalolin sauyin yanayin da gaggawa za kuma ta cimma kudirorin da ta sanya a gaba nan shekara ta 2030.  

"Ya ce sauyin yanayi batu ne na kariyar dan Adam, batu ne na kariyar tattalin arziki, batu ne kuma na kare muhallinmu, batu ne na tsaron kasa, kuma batu ne na bada kariya ga rayuwa a doron kasa".

Ya  baiyana yadda Amirka ke tunkarar matsalolin sauyin yanayin da matukar muhimmanci yana mai cewa tun daga lokacin da ya shiga ofis a ranar farko gwamnatinsa ta jagoranci daukar muhimman matakai don magance matsalolin muhalli a cikin gida da kuma sauran sassan duniya. Kuma ba tare da bata lokaci ba ya sake mayar da kasar cikin yarjejeniyar kare sauyin yanayi ta birnin Paris. Ya nemi afuwa game da fitar da Amirka ta yi daga yarjejeniyar a baya.