SiyasaAmurka
Biden: Kwaskwarima ga kotun kolin Amurka
July 29, 2024Talla
Shugaban Amurka Joe Biden a wannan Litinin zai gabatar da wasu shawarwari na garanbawul ga kotun kolin Amurka da alkalai yan mazan jiya suka fi rinjaye a cikinta.
Shawarwarin za su hada da takaita wa'adi da ka'idojin da'a ga alkalan kotun su tara wadanda ke aiki na dundundun har tsawon rayuwa.
Ana dai kyautata zato da wuya a amince da dokar yayin da kawunan yan majalisar ke rarrabe kuma kwanaki 99 suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka.