Berlusconi ya yi watsi da hukuncin da kotun Italiya ta yanke masa | Labarai | DW | 27.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Berlusconi ya yi watsi da hukuncin da kotun Italiya ta yanke masa

Tsohon shugaban gwamnatin Italiya Berlusconi ya mayar da martani kan hukuncin da aka yanke masa, tare da cewa zai ci gaba da siyasa.

Tsohon Firaministan kasar Italiya Silvio Berlusconi, ya facaccaki hukuncin da aka yanke masa kan kaucewa biyan kuɗaden haraji, sannan ya ce zai ci gaba da harƙoƙin siyasa har iya rayuwarsa, domin kawo sauyi ga ɓangaren shariyar ƙasar. Amma ya kawar da yuwuwar ya sake takaran mukamun firaminista yayin zaben shekara mai zuwa.

A cikin martanin da ya mayar, Berlusconi, ya kuma soki matakin da mutumin da ya gaje shi Mario Manti ya ɗauka, tare da shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel, kan tsuke bakin aljuhu.

Yayin taron manema labarai a birnin Milan, tsohon firaminista Silvio Berlusconi na ƙasar ta Italiya, ya ƙara da cewa, gamayyar jam'iyyu masu mulki za su sake duba goyon bayan da su ke baiwa gwamnatin firaminista Monti. Sannan kuma ya ce, za su ɗaukaka ƙarar hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da aka yanke masa kan kaucewa biyan kuɗaɗen haraji.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Awal Balarabe