Berlusconi ya shiga uku | Labarai | DW | 26.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Berlusconi ya shiga uku

Wata kotu a Italiya ta yanke wa tsohon firaiministan ƙasar, Silvio Berlusconi hukuncin ɗauri na shekaru huɗu a gidan yari bisa laifin kauce wa biyan haraji.

Laifukan da ake zargin tsohon firaiministn da aikatawa sun kuma haɗa ne da ƙayyade farashi ba akan kaida a kamfainsa na yada labaru. To sai dai ana dasa ayar tambaya game da ƙarfafa wannan hukunci a kotun daukaka kara saboda cewa tun wasu shekaru da suka gabata ne ya aikata wannan laifi. Kungiyar lauyoyin kasar ta Italiya ce ta shigar da bukatar yanke wa tsohon firaiministan mai shekaru 76 hukuncin ɗauri na shekaru uku da watanni takwas. Shi dai Berlusconi ɗaya ne daga cikin mutane da aka shigar da wannan ƙara akan su tun watannin shida da suka gabata. Ana zargensa ne da hannu a cikin wata harkar da aka kulla a shekarun 1990 ba a kan ƙaida ba- laifin da ya sake jaddada cewa shi bai aikata ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal