Berlusconi ya karfafa goyon baya ga shugaba Bush | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Berlusconi ya karfafa goyon baya ga shugaba Bush

Duk da kalaman da yayi baya-bayan nan na sukar yakin Iraqi, FM Italiya Silvio Berlusconi ya sake karfafa goyon bayansa ga shugaban Amirka GWB. A lokacin da yake magana a wata ziyara da ya kai fadar White House Berlusconi ya yabawa shugabancin Bush. Shi kuma a na sa bangaren Bush ya kira Berlusconi a matsayin wani babban aboki sannan ya bayyana dangantaka tsakanin kasashen su biyu da cewa kwakkwara ce. Jim kadan gabanin ya kai ziyarar birnin Washington, Berlusconi ya fadawa wata tashar telebijin Italiya cewa a lokuta da dama ya yi kokarin shawo kan shugaba Bush da ka da ya kaiwa Iraqi hari. Italiya dai na matsayin wata babbar kawar Amirka.