Beljiyam na fuskantar barazanar ta′addanci | Labarai | DW | 21.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Beljiyam na fuskantar barazanar ta'addanci

Hukumomi sun tsaurara matakan tsaro a Bruselles sakamakon babbar barazana ta kai hari da birnin ke fuskanta daga masu kaifin kishin Islama.

Gwamnatin Beljiyam ta nanata cewar wasu 'yan ta'adda na shirin kai wani mummunan harin kunar baki wake a Bruselles babban birnin kasar. Wannan dalilin ne ya sa ta dauki matakan tsaro mafi tsauri don hana faruwar harin a cewar Firimiyan kasar Charles Michel.

Cibiyar tattara bayanai kan ayyukan ta'addanci ta yi kira ga mazauna Bruselles da su guje ma wurare masu cunkoson jama'a ciki har da kasuwanni. Sannan kuma an rufe tashoshin jiragen kasa tare da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na gwamnati.

Ita dai Beljiyam ta na sahun gaba na kasashen da ke bayar da hadin kai wajen murkushe wadanda ke da hannu a tagwayen hare-haren birnin Paris na Faransa. Sannan kuma wanda ya kitsa wadannan hare-hare haifaffen kasar ta Beljiyam ne.

Kotun Beljiyam ta bayyana cewar ta gano makamai a gidan daya daga cikin wadanda take zargi, ba tare da bayyana ko wadanne ne ba. An dai kama wannan mutum ne tun ranar Alhamis da ta gabata a wani samame da aka kaddamar bayan harin birnin Paris.