Beji Essebsi ne sabon shugaban Tunisiya | Labarai | DW | 22.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Beji Essebsi ne sabon shugaban Tunisiya

Hukumar zaben kasar Tunisiya ta sanar da Mohamed Beji Caid Essebsi a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu zaben shugaban kasar.

Mr. Essebsi dai ya samu nasara a zaben ne da kashi 55.6 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben ta bayyana wanda ke nuna irin nasarar da ya samu kan abokin hamayyarsa Moncef Marzouki.

Tuni dai Marzouki din ta bakin kakakinsa ya taya Mr. Essebsi murnan samun nasara a wani sako da ya sanya a shafinsa na Facebook, yayin da kasashen duniya ke taya al'ummar Tunisiya murnar kammala komawa tafarkin dimokradiyya.

Wannan zaben dai shi ne irinsa na farko da aka gudanar tun bayan juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Zainul Abideen Bn Ali.