Bazuwar ′yan Jahadi a yakin Siriya | Siyasa | DW | 19.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bazuwar 'yan Jahadi a yakin Siriya

Masana sun bayyana fargabar cewa kungiyoyin masu zafin bin addinin na kan mamaye tawayen Siriya.

FILE - In this Friday, Jan. 11, 2013 file citizen journalism image provided by Edlib News Network, ENN, which has been authenticated based on its contents and other AP reporting, shows rebels from al-Qaida affiliated Jabhat al-Nusra waving their brigade flag as they step on the top of a Syrian air force helicopter, at Taftanaz air base that was captured by the rebels, in Idlib province, northern Syria. The Arabic words on the flag reads: There is no God only God and Mohamad his prophet, Jabhat al-Nusra. Last month, militants inside Iraq killed 48 Syrian government troops who had sought refuge from the war in their country _ an ambush that regional officials now say is evidence of a growing cross-border alliance between two powerful Sunni jihadi groups _ Al-Qaida in Iraq and the Nusra Front in Syria. The U.S. designates both as terrorist organizations, and the purported alliance is further complicating the equation for the West as it weighs how much to support the rebel movement.(AP Photo/Edlib News Network ENN, File)

Syrien Bürgerkrieg Kämpfer von Al Nusra Front

Yakin basasan kasar Siriya na ci gaba da janyo masu kaifin kishin addinin Islama, wadanda ke shiga domin aiwatar da manufar Jahadi. Tuni 'yan Jahadin suka mamaye rundunonin 'yan tawaye cikin sassa daban-daban na kasar. Inda aka bayyana cewa a yanzu dubban masu ikirarin Jahadi daga kasashen duniya suka kwarara domin tallafa wa 'yan adawa da ke neman kifar da gwamnati shugaba Bashar al-Assad.

***ACHTUNG: NICHT MEHR NACH DEM 02.10.13 NUTZEN (aus rechtlichen Gründen)**** Free Syrian Army members accompanied by fighters from the Islamist Syrian rebel group Jabhat al-Nusra carry their weapons as they stand in front of a damaged building in the old city of Homs July 2, 2013. Picture taken July 2, 2013. REUTERS/Mohamed Ibrahim/Shaam News Network/Handout via Reuters (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) ATTENTION EDITORS - THIS PICTURE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. REUTERS IS UNABLE TO INDEPENDENTLY VERIFY THE AUTHENTICITY, CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS IMAGE. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS.

Mayakan Jahadi a Siriya

Michael Stephens dan kasar Birtaniya na cikin wata kungiya mai zaman kanta, wadda ke kula da abin da ke faruwa cikin kasar ta Siriya, musamman yadda 'yan jahadi ke mamaye rundinonin 'yan tawaye:

"Ina ganin akwai kimanin mayakan Islama 60.000, kuma kimanin 2,000 zuwa 3,000 ne abin tsoro, wadanda su ke da tsananin ra'ayi da za a nuna damuwa. Amma kuma wannan adadi na 2,000 zuwa 3,000 abu ne mai yawa"

Mafi yawan wadan nan mayaka na Jahadi da ke kai gudumawa cikin yakin basasan kasar ta Siriya, sun fito ne daga kasashen ketere. Michael Stephens ya yi karin haske kan yankunan da wasu daga ciki su ka fito:

ARCHIV - Eine maronitische Kirche (vorne) und eine islamische Moschee, aufgenommen in der syrischen Stadt Maalula (Archivfoto vom 26.10.2005). Das Dorf Maalula ist die einzige Stadt in Syrien mit einer christlichen Mehrheit in der Bevölkerung. Im Libanon, in Syrien und in Jordanien, wo arabische Katholiken, Protestanten und Orthodoxe leben, ist es relativ einfach, eine Bewilligung für den Bau einer Kirche zu erhalten. Mit Abstand am schwierigsten ist die Lage im islamischen Königreich Saudi-Arabien, wo es keine einheimischen Christen gibt und der Bau von Kirchen strikt verboten ist. Foto: Oliver Berg (zu dpa-Korr. Kirchenerbauer haben es in der arabischen Welt nicht immer leicht vom 03.06.2007) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Kauyen Ma'alula a Siriya da ke da Coci da Masallaci a hade

"Mun san cewa daruruwa sun fito daga arewacin Turai, akwai shaidar cewa wasu sun fito daga birnin Hamburg na arewacin Jamus, wasu daga kasar Denmark, da ga Sweden, da ga Holland inda ake tura mutane da sunan kungiya. Suna haduwa a kudancin kasar Turkiya, daga nan suke shiga biranen Siriya na Aleppo ko Idlib"

Daya daga cikin kungiyoyin da ake tsoro kuma ake dangantawa da kungiyar al-Ka'ida, ita ce Al-Nusra. Ana daukan kungiyar a matsayin mai nuna rashin imani. Michael Stephens ya ce 'yan kungiyar tsiraru ne cikin rikicin.

"Kididdiga ta nuna yawan 'yan kungiyar Al-Nusra sun kai 5,000. Ina tsammani adadin na da yawa"

Rikicin kasar ta Siriya na kara zafafa, inda masu ikirarin Jahadi ke kai ruwa rana da dakarun gwamnati masu biyayya ga mahukuntan birnin Damascus.

Paul Salem daraktan wata gidauniya ta Gabas ta Tsakiya, ya yi bayani kan dangantaka tsakanin 'yan Jahadin da mazauna garuruwan kasar.

U.S. Secretary of State John Kerry (L) and Russian Foreign Minister Sergei Lavrov shake hands after making statements following meetings regarding Syria, at a news conference in Geneva September 14, 2013. The United States and Russia have agreed on a proposal to eliminate Syria's chemical weapons arsenal, Kerry said on Saturday after nearly three days of talks with Lavrov. REUTERS/Larry Downing (SWITZERLAND - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

John Kerry na Amirka da Sergei Lavrov na Rasha, ke goruwa kan rikicin Siriya

"Babu wani tsaro, mazauna garuruwan sun amince da masu kaifin kishin addinin, ko sun saba da masu neman kafa sharia irin na Wahabiyawa. Da kafa tsarin kama-karya, shugaban tsagerun ke zama alkali, wajen aiwatar da shari'a, kamar yanke hanun ko fille kai, ta mummunar hanya"

Cikin wannan rikici na Siriya 'yan tawaye na samun tallafi daga kasashen Yammacin duniya, wadanda kiri-kiri suke nuna adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Kungiyar Free Siriya tana cikin kungiyoyin da ke samun tallafi, wanda kuma ke dasawa da kasashen na Yammacin duniya. Wadannan 'yan tawaye kan samu kudi da makamai da sauran kayayyakin da suke bukata, daga kasashe masu nuna adawa da gwamnatin kasar. Yayin da kasashe kamar Rasha da Iran ke ci gaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Mawallafa: Andreas Gorzewski / Suleiman Babayo

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin