Bayelsa: Aski ya zo gaban goshi | BATUTUWA | DW | 15.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Bayelsa: Aski ya zo gaban goshi

A wannan Asabar ne za'a gudanar da zabuka a jihohin Kogi da Bayelsa, tuni hukumar zabe mai zaman kanta da rundunar 'yan sanda sun bayyana cewa komai ya kammala kan zaben da tabbatar da tsaro ga jama'a

Duk da ya ke jam'iyyun siysasa fiye da talatin ne ake sa ran za su fafatawa a zaben jihar Bayelsta, masana na ganin fafatawar za ta fi zafi ne a tsakanin tsakanin jamiyyun APC mai mulki a Najeriya da PDP mai mulkin jahar ta Bayelsta duk da yake an samu wasu da dama daga cikin jamiyyu da suka narke don marawa ko dai jam'iyyar APC mai a dawa a jahar ko kuwa jam'iyyar PDP mai mulki baya.

Hukumar zabe dai mai zaman kanta a jahar ta nunar ta shirya tsaf don tara zaben, haka ita ma rundunar 'yan sanda ta nuna cewar ta tura jami'anta kusan dubu talatin da biyu ko bayan wasu dubban da aka karo daga makwabtan jihohi, domin ganin an tabbatar da tsaro kuma zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali

 Zabe mai tattare da kalubalai

 A yayin da ake dab da ranar zabe an bunduge wasu jami'an 'yan sanda da suka je aikin tabbatar da tsaro a garin Nembe da ke jihar sannan a baya bayannan kuma wasu 'yan bindiga sun bude wutar kan mai uwa da wabi a wani jerin gwano 'yan wata jam'iyya da ke son yin gangamin siyasa a jihar inda aka hallaka mutn shida.

Wadannan halayyar na nuni da cewa zaben da ake son gudanarwa a ranar Asabar 'yan siyasar na son tunkarar sa ba tare da kwanciyar hankali ba, duk da yarjejeniyar gabanin zabe da wakilan jam'iyyun kasar suka rattaba wa hannu domin ganin an shirya zaben a tsanak, tare da tabbatar da dorewar hakan a bayan zabe.

Mr Nenge James, na daya daga shugabannin kungiyoyin sa kai da ke dakon kallon yadda zaben zai kaya,kuma dan asalin garin Nembe ne wato inda aka hallaka 'yan sanda biyu ya bayyana cewa suna kokarinsu domin ganin an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali.

Wani garari kuma da ya afkawa jamiyyar APC a jihar shine na yadda wata kotu ta yanke wani hukuncin hana dan takarar mataimakin gwamnan shiga zaben bisa dalilan yayi karya a shedar karatunsa koda yake yanzu jamiyyar APC tace babu wata damuwa domin ita ma ta garzaya wata kotu don dakatar da wannan hukunci kafin kaiwa ga maslaha tare kuma da jaddada cewar dan takarar na mataimakin gwamna zai iya shiga zaben. 

Shigo da 'yan sara suka daga waje

 Bayanai dai sun tabbatar da cewa wasu 'yan siyasa a jihar sun auno matasa 'yan jagaliyar siyasa daga makwabtan jihohi,da daga dukkanin alamu domin su tayar da hankullan jama'a a yayin yayin zaben haka suma jami'an zabe sai an sanya ido akansu a cewar bayyanai bisa zarginsu da hada kai da wasu 'yan siysasa a jihar don aiwatar da magudi, kana kuma hukumar 'yan sanda ta tura manyan jami'anta 20 a wasu wuraren domin saka ido kan yadda jami'an na 'yan sanda suke tafiyar da aikinsu na tsaro.

 Duk da halin da ake ciki na fargabar abinda kan je ya zo a zukatan masu zabe a jihar Bayelsa har yanzu akwai kyakyawan fata daga jama'a na cewar a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali domin zabar wanda zai shiga a gidan gwamnati na Creek Haven da ke Jihar.

Sauti da bidiyo akan labarin