Batun zabe a wasu kasashen Afirka ya mamaye jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 04.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Batun zabe a wasu kasashen Afirka ya mamaye jaridun Jamus

Galibi jaridun Jamus sun mayar da hankali a kan zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a kasar Senegal da ke a yankin yammacin Afirka.

Mafi yawan jaridun Jamus sun mayar da hankali ne a kann zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a kasar Senegal da ke a yankin yammacin Afirka. Jaridar Neue Zürcher Zeitung  ta yi sharhi mai taken "gamayyar jam'iyyun da ke mulki ta lashe zaben 'yan majalisa", jaridar ta yabawa zaben da ya dauki hankalin masu sharhi kan lamuran siyasa.Jaridar ta ci gaba da cewar, hadin kan jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi da  ke da akidar kasuwanci a karkashin jagorancin shugaba Macky Sall, ta samu gagarumar nasara. Bayan kwarya kwaryar sakamakon zaben, fraiminisa mai ci Mohamed Bin Abdallah Dionne a karkashin jam'iyyar hadakar ta BBY ta samu kujeru 42 daga cikin 45 da aka yi takararsu a ranar Lahadin da ta gabata. Zaben da ke zama zakaran gwajin dafi ga na shugaban kasa da ke zuwa a cikin watan Julin shekara ta 2019.Abokin adawa kuma tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade mutumin da ya yi kememe akan karagar mulki duk da kayen da ya sha a shekara ta 12, ya zo ya zame kadangaren bakin tulu a zaben na ranar Lahadi. Mai shekaru 91 da haihuwa, Wade ba shi da niyyar tsayawa takara. Sai dai ganin cewar har yanzu yana da dumbin magoya baya a Senegal, ya yi tattaki daga Paris zuwa Dakar domin marawa Karim baya.

Zaben kasar Ruwanda

Ita kuwa jaridar Süddeusche Zeitung tsokaci ta yi game da zaben kasar Ruwanda na wannan Juma'a. A taken labarinta da ke cewar " duk da cewar a karkashin shugaba Kagame Ruwanda ta samu bunkasa har ta na jan masu zuba jari zuwa cikin kasar, akwai wasu batutuwa da har yanzu kasar ke fama da su, duk kuwa da cewar ko shakka babu shi ne mai nasara a zaben na wannan Juma'a". Jaridar ta ci gaba da cewar har yanzu ana iya bayyana Ruwanda da kasancewa kasa gurguwa, ganin cewar itace a jeri na 138 daga cikin kasashe 195 na duniya a fannin tattalin artziki. Kuma da yawan al'umma kusan miliyan 12 ko kusa ba ta jerin kasashen da suke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika. Sai dai duk da haka, zaben shugaban kasa a Ruwandan na daya daga cikin muhimman lamuran siyasar Afirka da duniya ta mayar da hankali a kai a wannan shekarar, ganin cewar ba wai Ruwandan ta kasance daya daga cikin kasashen da suka yi saurin farfadowa bayan yakin basasa ba, amma kasancewarta wadda ta samu gindin zama a tsakanin takwarorinta da ke kewayen manyan tabkuna da ke fama da rigingimu. Tun bayan kisan kare dangi na shekara ta 1994, jam'iyyar RPF ta karbi ragamar tafiyar da kasar. Jam'iyyar da ta samu tushe daga tsoffin sojojin tawaye, wadanda suka cimma nasarar kawo karshen kisan gilla da ake wa 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye, kuma a yau shugabanta Paul Kagame shi ne mutum mafi karfi a Ruwanda, wanda ke shugabanci tun daga shekara ta 2000, bayan rike kujerar mataimakin shugaban kasa da kuma ministan tsaro.