1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman lafiya a Afirka ya dauki hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
September 14, 2018

Matsalolin da rashin kwanciyar hankali ke janyo wa a wasu kasashen nahiyar Afirka, batutuwa ne da suke da bukatar hankalin da ya dace don kawo karshensu. Jaridun Jamus sun yi tsokaci game da su a sharhunan da suka yi.

https://p.dw.com/p/34sK4
Äthiopien Addias Ababa - Isaias Afwerki - Abiy Ahmed
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Ayene

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung da labarinta mai taken karin mataki a turbar samar da zaman lafiya a yankin Kahon Afirka.

Ta ce bayan wani yaki da zama gaba na tsawon shekaru 10 yanzu kasashen Jubuti da Iritiriya sun kama hanyar magance rikicin da take tsakaninsu. Tuni dai har an yi wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajen Jibuti Mahamud Ali Youssouf da takwaran aikinsa na Iritiriya Osman Saleh Mohammed, ganawar kuma da ta samu halartar takwarorinsu na Somaliya da Habasha.

Ganawar ta bude wani sabon babi na dangantaka tsakanin kasashen biyu. Rikicin kan iyaka da ya samo asali a 1996 lokacin da Iritiriya ta yi kokarin mamaye yankin Ras Doumeira na Jibuti, ya yi sanadi na ryukan mutane da yawa.

Asmara - Premierminister Abiy Ahmed mit somalischem Präsidenten Formajo und Präsident Isaias
Hoto: Prime Minister's Office/F. Arega

A 1999 da 2008 dakarun Iritiriya sun sake yin wani yunkuri na kwace yankin. Tun ba yau ba Jibuti ta yim kira ga kungiyar tarayyar Afirka AU da ta shiga tsakani. Ko da yake Jibuti karamar kasa ce amma tana taka muhimmiyar rawa saboda tashar jiragen ruwanta da kuma yankin da take.

A wannan shekara an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iritiriya da Habasha, ana kuma kyautatawa Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya taka rawa a sulhun da ake yi yanzu tsakanin Jibuti da Iritiriyar.

Tambaya a nan ita ce ko Abiy Ahmed zai shiga tsakani a kawo karshen rikici mafi girma a yankin na Kahon Afirka wato na kasar Somaliya.

Idan muke leka kasar Kamaru kuwa jaridar Die Tageszeitung ce ta yi hira da Christopher Fomunyoh wani dan kasar Kamaru wanda kuma shi ne darakta da ke kula da sashen Yammaci da Tsakiyar Afirka a Cibiyar Nazarin Mulkin Dimukuradiyya ta Kasa da ke birnin Washington.

Nigeria Wahlen Christoph Fomunyoh
Hoto: NDI

Jaridar ta Die Tageszeitung ta nemi sanin ra'ayinsa dangane da zaben da ake shirin gudanar a Kamaru a ranar 7 ga watan Oktoba, musamman saboda rikicin da ake yi a yankin nan na masu amfani da harshen Ingilishi. Masanin ya fara ne da cewa rikicin yankin na Aglophone na zama wani zakaran gwajin dafi na zaman Kamaru kasa daya al'umma daya.

Saboda rikicin ya ce shim kam da ya so shugaban kasa Paul Biya wanda tun a 1982 yake kan mulki, ya ba da fifiko wajen magance rikicin kafin a yi batun shirya zabe. Ya ce ba ya jin za a iya gudanar da zabe a yankin mai fama da rikici. Ya ce idan zabukan suka gudana a yankunan masu amfani da harshen Faransanci kawai, rikicin zai kara yin muni.

A karshe sai jaridar Kölner Stadt-Anzeiger wadda ta yi tsokaci a kan bikin nuna fina-finan Afirka karo na 16 a birnin Kwalan tana mai cewa bikin da ke fito da ainihin abubuwa na boye a Afirka, yana taka muhimmiyar rawa wajen nuna wa duniya fuskoki dabam-dabam na Afirka ba kawai matsaloli na yunwa da fatara da yake-yake da bala'o'i da a kullum ake alakanta su da nahiyar ta Afirka ba.