Batun ci-rani na ci gaba da zama matsala a Moroko | Siyasa | DW | 23.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Batun ci-rani na ci gaba da zama matsala a Moroko

Miliyoyin matasan kasar Moroko ne ke neman ketarawa zuwa nahiyar Turai. Sai dai yanzu ita ma kanta kasar na karbar 'yan ci-rani daga kasashen Afirka Kudu da Sahara.

Kasar ta Maroko dai na cewa tana son taimaka wa 'yan uwanta na Afirka amma a daya hannun tana aikin hadin kai da kungiyar EU wajen kiyaye kan iyakokinta daga kwararar 'yan ci-rani. Kasar ta sha musanta zargin da ake mata na zama Jandarmar kasashen Turai a bangaren yaki da 'yan ci-rani.

To ko me ya sa yanzu ake samun yawan bakin haure da ke tsallakawa kasar Spaniya daga Maroko? Na daya ana yada labarin cewa tun a 2014 zuwa 2015 bakin haure da 'yan gudun hijira na da kyakkyawar damar samun izinin zama a Turai. Na biyu aikin ceto a tekun Bahr Rum ya sa da yawa na wkarin gwiwar cewa ana iya cetonsu daga teku, sannan na uku a cewar jami'in shi ne masu fasakaurin miyagun kwayoyi na yi wa 'yan gudun hijira alkawarin kai su Turai daga Maroko a banza.

Wani yaro dan shekaru 14 da aka sakaya sunanshi, dan Maroko ne da ya kaura daga garin Fes zuwa birnin Tanger mai tashar jiragen ruwa, daga nan ana iya hango gabar tekun kasar Spaniya. Ya ce burinsa shi ne ya tafi Spaniya. Tun yana da shekara 11 ya bar gida saboda azabar da ya sha a hannun mijin mahaifiyarsa.

Ya ce: "A gani-na can ta fi Maroko kyau. A can za su ba ka masauki da kayan sawa da abinci, sannan bugu da kari a ba ka ilimi. Amma a Maroko cibiyoyin ajiye yara da matasa sun zama kamar gidan kurkuku, za a ci zarafinka, babu isasshen abinci."

Su ma 'yan kasashen Afirka kudu da Sahara da suka tsere wa rigingimu da matsaloli na talauci da fatara suka shiga Maroko suna neman sa'ar tsallakawa Turan. Wannan na zama matsala ga Maroko. An zargi jami'an tsaron kasar da take hakin dan Adam lokacin da suka kai samame da nufin korar bakin hauren daga arewaci zuwa kudancin kasar.

Sai dai ma'akatar cikin gida ta musanta wannan zargi, hasali ma Maroko ta ba wa bakin haure fiye da dubu 10 izinin zama cikin kasar a cewar wani babban jami'i a ma'aikatar cikin gida, Khalid Zerouali. A halin da ake ciki yawan yara masu karancin shekaru daga yammacinn Afirka da ma 'yan kasar Maroko da ke son zuwa Spaniya ya karu.

A kasashen EU irinsu Spaniya da Faransa da Jamus ba a korar yara kanana da suka shiga kasashen su kadai. Maroko dai ta ce ana bukatar cikakken hadin kai da daukar matakai na bai daya tsakanin Afirka da Turai matukar ana son a magance wannan matsala.

Sauti da bidiyo akan labarin