Basaraken Zulu na Afirka ta Kudu ya yi amai ya lashe
April 20, 2015Talla
A ranar Litinin ɗin nan sarkin Zulu mai ƙarfin faɗa a ji a ƙasar Afirka ta Kudu Goodwill Zwelithini ya yi amai ya lashe inda ya bayyana farmaki da aka kai wa baƙi a ƙasar da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane bakwai cikin wannan wata da cewa abin takaici ne kuma ba dai dai ba ne.
Shi dai basarake Zwelithini ana zarginsa da zama kan gaba wajen rurra wutar rikici da ma harzuƙa ƙyamar baƙi a kasar ta Afirka ta Kudu bayan da wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta ɗauki kalamansa na cewar baƙi su fice daga ƙasar ta Afirka ta Kudu. Ya dai ce bayanansane ba a fahimta ba inda kuma ya yi Allah wadai da kai farmakin kan baƙi a ƙasar ta Afirka ta Kudu.