Barrow: Demokradiyya ta zauna a Afirka
January 21, 2017Talla
Barrow na magana ne, a daidai lokacin da tsohon shugaba Yahya Jammeh ke shirin tattara yanasa yanasa ya fice daga kasar.
Barrow ya ce " abu ne mai muhimanci. Ina ganin demokradiyyar na samun gindin zama a Afirka, kuma hakan babban cigaba ne. Sauyi ne mai kyau wa Afirka. Kuma hakan zai yi tasiri a nahiyar".
Bayan tattaunawa na tsawon lokaci da shugabannin yankin yammacin Afirka, da barazanar yiwuwar amfani da karfin soji a kansa, da safiyar wannan Asabar din ce Yahya Jammeh ya sanar da cewar zai sauka daga mulki.
Sai dai har yanzu ba'a sanar da ranar da shugaba Barrowzai bar Dakar inda ya sha rantsuwar karbar mulki, zuwa Banjul babban birnin kasarsa ta Gambiya ba.