Barazanar zazzabin cizon sauro a Najeriya | Zamantakewa | DW | 11.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Barazanar zazzabin cizon sauro a Najeriya

Hukumar kula da kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa da za a samu isassun kudade na gudanar da ayyukan yaki da cutar Malariya da za a iya ceto rayukan mutane sama da dubu 10 a Najeriya.

Hukumar kula da kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa in da za a samu isassun kudade na gudanar da ayyukan yaki da cutar Malariya da za a iya ceton rayukan mutane sama da dubu 10 a Najeriya. Mutane kimanin miliyan uku da dubu 700 ne su ke neman taimakon agaji na ayyukan jin kai wanda kuma dukkanin su ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wanda aka fi sani da Malaria.

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayyana cewa tun daga watan Oktoba shekarar da ta gabata akwai kimanin mutane dubu takwas da dari biyar da ke kamuwa da cutar a kowane mako inda ake sa ran alkaluman za su fi haka a nan gaba. Rahotan na hukumar lafiya ta duniya ya kuma nuna cewa sama da rabin mace-mace da ake samu a tsakanin 'yan gudun hijirar a sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro ne wannan ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta himmatu wajen yakar cutar ta hanyar raba gidajen sauro da kuma raba magungunan riga-kafi na kamuwa da cutar zazzabin don dakile barnar da za ta yi. 

Sauti da bidiyo akan labarin