1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar 'yan tawayen Afirka ta tsakiya

December 31, 2012

'Yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun yi barazanar kutsawa Bangui babban birni idan gwamnati ba ta daina musgunawa fararen hula da kuma magoya bayansu ba.

https://p.dw.com/p/17Baa
Hoto: AFP/Getty Images

Hadeddiyar Kungiyar 'yan tawayen ta Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da aka fi sani da suna Seleka ta zargi gwamnati da kashe fursunoni ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Kana ta nunar da cewa shugaba Bozize na takurawa mazauna Bangui da ke adawa da manufofin mulkinsa. Saboda haka ne ta nemi dakarun Kungiyar tsaro na yankin tsakiyar Afirka wato CEEAC da ke shiga tsakani da su tabbatar da lafiya da kuma dukiyoyin mazauna Bangui babban birni, ko kuma su yi gaban kansu: Ma'ana su kutsa birni domin kawo karshen abin da suka kira cin zali tare da kawo karshen mulkin shugaba Francois Bozize.

Francois Bozize Zentral Afrika
Sojojin gwamnati na ci gaba da kare BozizeHoto: AFP/Getty Images

Rundunar FOMAC ta kasashen tsakaiyar Afirka wadda ke da cibiyarta a Damara da ke da tazarar kilometa 75 da Bangui ta kara yawan dakarunta a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya tun a karshen mako. Kana sojojin gwamnati na ci gaba da daura damara domin kare babban birnin daga farmaki 'yan tawaye. Lamarin da Souleymanou Sani da ke zama mazaunin Bangui ya sanya zullumi a zukatan al'uma.

Shugaba François Bozize ya yi alkawarin kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi bangaori daban daban na kasar ciki kuwa har da 'yan tawaye, tare da sauka daga kujerar mulki idan wa'adinsa ya cika. Kana a lokacin da ya gana da shugaban Benin, kana shugaban kungiyar Gamayyar Afirka Thomas Boni Yayi, shugaban na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya ce a shirye ya hau kan teburin tattauna da 'yan tawayen Seleka a birnin Libreville na Gabon ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai kuma 'yan tawaye da kuma 'yan adawan kasar su mayar da martani a inda suka bayyana shakkun game da tayi Bozize. Madugun 'yan adawan kasar Martin Ziguele ya bayyana cewa Bozize ya saba yin alkawaru da ba ya cikawa kamar yarjejeniyoyin da aka cimma da shi a baya. Su ma 'yan tawayen Seleka sun nuna dari-dari da kiran shugaba na Afirka ta tsakiya. Kana sun zarge shi da shirya kai musu farmaki a garuruwan da ke karkashin ikonsu. Amma kuma a ranar asabar sai dai hadeddiyar kungiyar tawayen Seleka ta fatattakin sojojin gwamnati a lokacin da suka yi fito na fito da su a Bambari. A cewar Souleymanou Sani rashin shawo kan matsalar tawaye daga bangaren gwamnati ba ya rasa nasaba da rarrabuwar kawuna da ake fiskanta a tsakanin sojojin kasar.

Zentralafrikanische Republik Stadt Zentrum von Bangui
Tawaye ya sa Bangui tafiyar hawainiya.Hoto: DW/Leclerc

Duk da alkawarin hawa kan teburin sulhu da kungiyar Seleka ta yi, amma kuma akasarin manyan biranen kasar na ci gaba da zama karkashin ikonta. Seleka Ta na neman shugaba Francois Bozize ya mutunta yarjejniyoyin 2007 da kuma na 2011 da suka cimma tsakaninsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal