Barazanar tashin Bom a taron Fifa
May 29, 2015An fuskanci barazanar tashin bom a cibiyar hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta duniya wato FIFA dake a birnin Zurick na kasar Switzerland.Lamarin ya wakanan ne a daidai lokacin da hukumar ke gudanar da babban zaman taron congres dinta a ranar juma'a domin zaben sabon shugabanta.Wani babban jami'in hukumar yan sanda ta kasar ya tabbatar da fuskantar barazanar tashin bom din.
Masu aiko da rahotanni sun ce yanzu haka bayan da aka fito cin abinci daga zauran taron ba a baiwa mahalartan ba izinin sake komawa a cikin zauran taron inda yanzu haka ake ci gaba da gudanar da bincike .Hukumar ta Fifa na gudanar da wanann taro ne na zaben sabon shugaban nata a cikin wani munmunan yanayi na zargin cin hanci da rashawa a tsakanin mambobin nata wadanda tuni aka kargame wasu daga cikinsu.