Barazanar komawa yaki a jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya
March 18, 2013A wannan Litinin ( 18. 03. 2013), 'yan tawayen jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya sun cafke wasu ministocin kasar guda biyar, wadanda aka baiwa mukamai cikin gwamnatin hadin kan kasar da aka samar, bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnati ta kulla tare da 'yan tawayen, kana 'yan tawayen sun yi barazanar komawa fagen yaki idan har hukumomin kasar ba su biya bukatunsu ba.
Ayarin ministoci biyar din ya tafi garin Sibut ne da ke arewacin Bangui, babban birnin kasar, a matsayin wani bangare na tawagar wakilan da za su gana tare da kawancen kungiyar 'yan tawaye ta Seleka domin tattauna hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yanda ministan kula da harkokin tsaron kasar ta jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya Josue Binoua ya fadi.
Shi kuwa kanal Djouma Narkoyo na rundunar 'yan tawayen, cewa yayi suna bukatar gwamnatin shugaba Francois Bozize, ta saki daukacin fursunonin siyasa, kana da gujewa tafiyar da majalisun ministoci biyu, da kuma mutunta tanade tanaden da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma kimanin watanni biyu da suka gabata.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas