1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Barazanar karancin abinci a nahiyar Afirka

Gazali Abdou Tasawa
September 6, 2018

Taron kwararru a fannin harkokin noma na Afirka da ya gudana a wannan mako a birnin Kigali ya yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi da kuma yaduwar tsutsotsi na barazanar haddasa matsalar karancin abinci a Afirka. 

https://p.dw.com/p/34RoP
Raupe von Papilio bianor
Hoto: cc-by-sa-Jörg Hempel

Kwararrun sun ce nau'in tsutsar nan zunkudau da ta samo asali daga kasashen Latin Amirka da kuma aka gano yaduwarta a kasashen Afirka a shekara ta 2016, yanzu haka na yaduwa kamar wutar daji inda tuni aka gano ta a kasashe 44 daga cikin kasashen nahiyar Afirka sabanin kasashe 28 a shekarar da ta gabata. 

Kwararrun sun kiyasta cewa mutane sama da miliyan 300 ne ka iya fuskantar barazanar karancin abinci a shekarar ta bana a sakamakon wannan tsutsa da sauran kwarin wanda babu wani nau'i na shuka da ba sa far ma wa.