Barazanar hare-hare a Kenya | Siyasa | DW | 18.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barazanar hare-hare a Kenya

Karuwar hare-haren ta'addanci na neman dagula al'amura a kasar Kenya, inda kuma hakan ke shafar walwalar 'yan kasa da baki

A kasar ta Kenya yanzu haka al'ummar na cikin zaman dar-dar bisa wadannan hare-haren 'yan ta'adda. Harin bayan nan da aka kai yankin da masu yawon shakatawa ke matukar ziyara, ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 65. Hakan ya zo ne 'yan watanni kafin zagayowar shekara guda da mummunan harin da aka kai kasuwar zamani ta Westgate a Nairobi babban birnin kasar. Kungiyar Al-shabaab ta kasar Somaliya ta yi ikirarin kai wandannan hare-hare bisa kutsen kasar Kenya a Somaliya.

A shekara ta 2006 ne dai kungiyoyin addini suka karbi madafun iko a Somaliya, sai dai watanni shida bayan suna mulki karkashin kungiyar kotunan Islama, sai kasar Habasha bisa goyon bayan Amirka ta aukawa Somaliya da yaki, inda aka wargaza kungiyoyin da suka kafa gwamnati a Mogadishu, abin da kuma ya sa suka rikide suka zama Al-shabaab. Bayan da al-shabaab suka yi karfi sun sake karbe kusan daukacin kasar Somaliya ciki har da fiye da rabin Mogadishu babban birnin kasar. Kungiyar ta kuma samu hada hannun da kungiyoyin jihadi a duniya. Kutsen da kasar Kenya ta yi a shekara ta 2011 don yakar Al-shaabab ya jawo mata mummanan martani. Sai dai gwamnatin Kenya ta ce babu abin da zai sa ta fice daga Somaliya, duk kuwa da barazanar da 'yan ta'addan ke yi wa Kenya. Kamar yadda Andrew Asamoah, da ke cibiyar nazarin harkokin tsaro a Pretoriya ya bayyana.

"Gwamnati ta ce ba za a tilasta mata ficewa daga Somaliya. Inda gwamnati ta sake nanatawa, 'yan ta'adda ba za su sa Kenya ta bar yakar ta'addanci ba, kuma ina ganin har yanzu shi ne matsayin gwamnati"

Shigar da dakarun kasar Kenya a Somaliya karkashin kungiyar Tarayyar Afirka ya ba da damar fatattakar kungiyar Al-shabab daga yankuna da dama, kama daga birnin Mogadishu har izuwa Kismaayo da ke da tashar jiragen ruwa, abin da kuma ya zama mummunar koma baya ga kungiyar Al-shabaab. Abin da kuma ya sa kungiyar Al-shabaab ta ci gaba da kai hare-hare cikin kasar ta Kenya.

To sai dai abin da ke a fili ba duk Musulman Kenya ba ne ke maraba da ayyukan kungiyar Al-shabab mai ikirarin yin jihadi. Kamar yadda sakatare janar na kungiyar majalisar Musulman Kenya Adan Wachu ke cewa.

"Babu abin da ya hada matakan kungiyar da Musulunci. Musulunci na Allah wadai da ta'addanci. Musulunci na tir da kisan dan Adama, dama duk halitta. Don haka duk mutumin da ya yi ikirarin yana haka da sunan Musulunci to ya sani hakan ba Musulunci ba ne. Domin kuwa addinin Musulunci na kyamar irin wadannan matakai"

Hare-haren da kungiyar Al-shabaab ke kai wa, da kuma irin tsauraren matakan da gwamnati ke dauka wajen mayar da martani, suna matukar yin barazana ga zaman lafiyar kasar, inda yanzu Musulman Kenya ke cikin zaman zullumi kan irin munanan matakan da jami'an tsaro suka dauka, a shirinsu na yaki da 'yan ta'adda.

Mawallafa: Philipp Sandner/ Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin