Barazanar cutar Ebola a kasashen Afirka ta dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Barazanar cutar Ebola a kasashen Afirka ta dauki hankalin jaridun Jamus

Cutar Ebola a kasashen Kwango da Yuganda ta dauki hankalin jaridun Jamus gami da hare-hare da aka samu a kasar Mali da ke yankin yamamcin Afirka.

Sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta mai take "Ebola ta farmaki Yuganda" Tsawon watanni cutar ta fara yado a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a yanzu annobar ta bulla a makwabciyar kasa ta Yuganda. Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, tana tunanin ayyana cutar a matsayin wadda ke bukatar matakin gaggawa a duniya.

Jaridar ta ce cutar da ke yin kisa cikin gaggawa ta shiga Yuganda cikin sirri, ta hanyar wasu iyalai da suka dawo gida daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Tun da fari mutane 14 ne daga iyali guda suka fara bulaguron, a yayin da suka iya kan iyaka 12 daga cikinsu sun nuna alamun kamuwa da cutar, abin da ya ankarar da jami'aan tsaron kan iyaka. Baki dayansu an killace su a cibiyar da aka tanada domin wadanda ake zargin suna dauke da kwayar cutar Ebolan.

Sai dai shida daga cikinsu sun tsere cikin gari a cikin jiragen kasa zuwa yankunan karkara a ranar da aka killace su. A washe gari aka akwantar da guda a asibitin kauyen Kagando. Wani yaro dan shekara biyar da ke cikin iyalan ya rasa ransa, daga bisani kakarsa ta bi shi. Sakamakon binciken da likitoci suka gudanar a kansa ya nuna Ebola ta isa Yuganda. Tuni dai aka yi wa likitoci da jami'an kiwon lafiya kimanin 5000 rigakafin cutar tare da ba su horo kan yadda za su kula da masu dauke da cutar ta Ebola.

Ramuwar gayya da mutuwa da koma baya a Mali, in ji jarida Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce kasashen Afirka da dama na dawur-dawur a waje guda. A daren Lahadi na makon da ya gabata ne, wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari kauyen 'yan kabilar Dogon da ke tsakiyar kasar Mali tare da halaka mutane kimanin 100.

Ana dai tunanin harin ramuwar gayya ne. Cikin watan Maris din da ya gabata 'yan kabilar ta Dogon sun halaka Fulani kimanin 160. Jaridar ta ce takun saka tsakanin manoma da makiyaya da kabilar Dogon da Fulani da kuma Musulmi da wadanda ba Musulmi ba ne asalin rikicin. Gwamnatin kasar ta Mali dai ta tsaya kai da fata cewa harin ta'addanci ne, sai dai hakan bai wadatar ba. Koda yake masu kaifin kishin addini da masu tsattsauran ra'ayi na taka muhimmiyar rawa, sai dai ba za a iya tantance na kwarai da bara gurbi ba a wannan rikicin.