Barazana kan ′yan jarida a Nijar | Siyasa | DW | 16.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Barazana kan 'yan jarida a Nijar

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin yada labaru masu zaman kansu da 'yan jarida na nuna damuwa game da yadda wasu jami'an tsaron kasar ke muzguna wa 'yan jarida da karbe kayayakin aikinsu.

Dan jarida a bakin aikinsa

Dan jarida a bakin aikinsa na daukar labarai a Nijar

Kungiyoyin sun ce wannan ba karamar barazana ba ce ga ‘yancin fadar albarkacin baki da na aikin jaridar wanda gwamnatin kasar ta rattaba wa hannu. Duk da matakan da hukumomin kolin kasar ke cewa suna dauka na kara inganta fannin aikin jarida da walwalar fadar albarkacin baki a mulkin demokradiyya, bai hana samun hatsaniya ba tsakanin bangaren ‘yan jaridun kasar musamman masu zaman kansu. 'Yan jaridun sun ce suna fuskantar turjiya da cin zarafi wasu lokutan daga jami’an tsaron da ke aikin kwantar da tarzoma ko zanga zanga, lamarin da a wannan karon ‘yan jaridun masu zaman kansu suka ce tura ta fara kaiwa bango. A cewarsu bangaren shari’a ce ba ya aikinsa saboda da a ce dan jarida ne ya taka dokar, da sai ka ji an kai shi a kotu don hukunta shi. ‘Yan jaridun na zargin a duk lokacin da suka fito suna aiki, sai a taka masu hakki yanda ake so amma kuma ba a cewa komai.

Niger Anti Charlie Hebdo Protest Polizeieinsatz 18.01.2015 (Boureima Hama/AFP/Getty Images)

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar

Lamarin baya-bayan nan da ya jibanci batun cin zarafi dai ya faru ne a ranar Litinin inda jami’an tsaro suka karbe wasu kayayyakin aiki na kafafen yada labaru masu zaman kansu da suka hada da gidan Rediyon Tenere da na Labari, a yayin da suke aikinsu na daukar labarin wata zanga-zangar lumana da daliban kasar suka gudanar inda aka yi ta dauki-ba-dadi tsakanin jami’an tsaron kasar na Garde Nationale da yan jaridun da ke fagen aiki. Wannan lamarin dai tuni ya fara daukar hankalin kungiyoyin kasa da kasa da ke kare hakkin ‘yan jaridu da ma na cikin gidan wadanda ke yi wa batun kallon wani sabon salo dake shirin mayar da hannun agogo baya.

Wasu dake ilmantuwa daga labarai a Nijar

Wasu dake ilmantuwa daga labarai a Nijar

 Ba tun yau ba ne dai kasar ta Nijar ta mallaki muhimman dokokin dake kare ‘yan jarida wanda shugaba Mouhamadou Issoufou, na daya daga cikin misali ga kasashen Afirka da ya rattaba hannu kan kudurin. Sai dai har yanzu tsarin nasa na ci gaba da fuskantar cikas, inda a kasa da shekaru biyu kawai fiye da kayan aikin gidajen Rediyo da talabijin na kasar 5 ne jam’an tsaro suka kwace, ciki har da gidan Redion Bonferey da Tenere da Labari da a ke yi wa kallon masu yin kakkausar suka ga gwamantin kasar.