Baraka a kungyiyoyin fafaren hula na Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 19.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Baraka a kungyiyoyin fafaren hula na Jamhuriyar Nijar

Wasu kungiyoyin fararen hula sun soki lamirin sabon hadin gwiwar kawancen 'yan adawa da kungiyoyin fararan hula da aka kafa da zimmar yakar muyagun manufofin gwamnatin kasar

A daura da manufofi da akidu na kare hakkin dan adam ko na kiyaye tafiyar demokaradiyya da kungiyoyin fararen hula ke yi a Jamhuriyar Nijar, dokoki da ka'idodin tafiyar kasar ba su hana wata ko wani rukunin jama'a ba haduwa da zummar zartar da manufofinsu na bunkasa kasa da wanzar da 'yancin dan adam ko kiyaye tafarkin demukradiya.

Kamar yadda aka gani a shekarun 1990 kafin kiran wani babban taron kolin kasar da ake kira Conférence Nationle ko kuwa a jamhuriya ta hudu a yayin gwamnatin Marigayi Ibrahim Bare Mainassara ko abin da ya afku a baya-bayan nan a shekarun 2010 a yayin da gwamantin hambararen shugaban kasa Mouhamadou Tandja.Sai dai sabon kawancen da aka kafa mai launin FPR bai kasance wani abin mamaki ba ga kungiyoyi da ma masu bibiyar al'amurran yau da kullum na kasar domin tarihi ya nuna cewa a duk lokacin da wasu ke son gwagwrmaya dole sai sun hada karfi da karfe walau na neman mulki ne ko na tabbatar da 'yanci da walwalar dan adam. Sai dai tuni wasu 'yan fararen hula da suka cewa kawancen a kai kasuwa suka fara sukar sabon kawancen mai suna FPR.


Wata barakar kuma da aka lura da ita a yayin da Nijar ke shirin shiga zabe shi ne na yawaitar kungiyoyin fararen hullar da suka ce za su kasa su tsare su raka domin ganin an gudnar da zabe a cikin adalci.

Sauti da bidiyo akan labarin