Bankwana da tashar DW a Kigali | Zamantakewa | DW | 01.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bankwana da tashar DW a Kigali

A ranar 29 ga watan Maris aka rufe tashar watsa shirye-shiryen Deutsche Welle ga kasashen Afirka da ke Kigali babban birnin kasar Ruwanda.

A karshen mako tarihin wani bangaren watsa shirye-shiryen rediyo ya kawo karshe, inda aka rufe tashar watsa shirye-shiryen Deutsche Welle ta karshe a ketare. Tun a shekarar 1965 tashar da ke Kigali babban birnin kasar Ruwanda ta ke watsa shirye-shiryen Deutsche Welle zuwa kasashen nahiyar Afirka ta gajeren zango. Amma yanzu an rufe tashar daidai lokacin bikin cikarta shekaru 50 tana aiki a kasar ta Ruwanda.

Tashar da ke birnin na Kigali da ke karba kuma ta watsa shirye-shiryen Deutsche Welle ga kasashen Afirka ta gajeren zango, ga ma'aikatanta kam ta zama wani bangare na rayuwar Jamus a wata kasa mai nisa, ta kuma kasance wani tarihi mai sosa rai ga ma'aikatanta 'yan kasar Ruwanda.

Kwanaki kadan gabanin a rufe tashar a Kigali, Injiniya Dietmar Wolf ya yi karin haske.

"Za a rusa ginin tashar. Ba za mu kara yin amfani da ita ba. Za a kwashe kayan da ke ciki gaba daya a zubar."

Walter Berger da ke a birnin Kwalan yanzu bayan ya yi ritaya, ya kasance na farkon wadanda suka gina tashar a Kigali shekaru 50 da suka gabata. Ya ce rufe tashar tamkar cire masa wani bangare na tarihin rayuwarsa ne.

"Zan iya cewa yanzu haka kwalla nake yi, domin tashar ta kasance wani abin da muka gina shekaru 50 da suka wuce. Ta kasance wata karamar aljanna a gare mu."

Ruwanda a shekarar 1963

Shekara guda bayan Ruwanda ta samu 'yancin kai, sabuwar gwamnati a Kigali ta kulla yarjejeniyar da Deutsche Welle da ta ba wa tashar da ke watsa shirye-shirye daga Jamus zuwa ketare, tafiyar da aikin tashar a Kigali babban birnin Ruwanda. Daga na su bangaren Jamusawan sun taimaka aka gina gidan rediyon Ruwanda wato "Radio Ruanda"

Relaisstation Kigali

Ma'aikata na biki gabanin fara aikin tashar a 1965

Tashar ita ce tashar karba da watsa shirye-shirye ta farko da DW ta gina. A shekarar ta 1963 lokacin Walter Berger na da shekaru 21 ya kasance cikin injiniyoyin da suka gina tashar. Ya tuna lokacin da ya fara zuwa Ruwanda.

"1963, a lokacin ba masu zuwa yawon bude ido da yawa. Akwai mai daukar hoto a gaban tashar, wanda ke daukar hoton masu fitowa daga sassa daban-daban na duniya don gane wa idonsu aikin da muke yi. Mun dasa bishiyoyi kana mun kakkafa eriya da muka yi amfani da su wajen watsa shirye-shiryen."

Kyakkyawan yanayin aiki a tashar

A ranar 24 ga watan Oktoban 1965 tashar a Kigali ta fara watsa shirye-shirye ta gajeren zango.

An kafa eriyoyi tsakanin bishiyoyi kuma tun daga tsakiyar birnin Kigali ana hango tashar domin babbar eriya din a kan tsaunin Kininya aka kafa ta. Sannu a hankali an kammala ginin ofisoshin da kuma gidan ma'aikata Jamusawa da 'yan Ruwanda. Kasance babu katanga da ta kare ginin, dabbobi irin birarrai da sauransu sun yi ta kutse cikin tashar, inji Peter Stabusch wanda a karshen shekarun 1960 a karon farko ya je Kigali a matsayin injiniya, wanda ya kara da cewa an samu kyakkyawan yanayin aiki.

"Kai tsaye dabbobi kan shigo mana. Wani lokacin muna ganinsu a cikin akwatunan kayakin da muka sayo daga gari. Dole ka kasance cikin tsanaki. Mun samu kyakkyawan yanayin aiki tsakaninmu da 'yan kasa. Mun zama tamkar 'yan uwan juna."

Rousette Berger 'yar kasar ta Ruwanda ce ita ma ta ce an yi zaman girma da arziki da abokan aikin a Kigali. Ta yi aiki a matsayin sakatariyar daraktan tashar.

"Mun yi aiki cikin jin dadi da annashuwa. Mun kasance tamkar iyali daya. Na yi hulda da 'yan Afirka da Turawa. Yanayin da muka samu kanmu a ciki a wancan lokaci ya yi daidai da wata zamantakewar iyali daga al'adu daban-daban."

A cikin shekarun 1970 da 1980 injiniyoyin a tashar sun sha da kyar wajen samun shirye-shiryen na DW ba tare da wata matsala ba, domin yakin cacar baka a lokacin ya kuma shafi fasahar watsa labarai ta tashoshin gajeren zango. Kasashen gabashi sun yi ta kokarin yin kutse a hanyoyin watsa shirye shirye na DW. Peter Stabusch injiniya a tashar ta Kigali ya yi karin haske.

"Su ma masu saurare sun gane abin ke tafiya. Sai sun yi da kyar kafin su iya kama tashar Deutsche Welle, amma sai kuma ta dauke bayan wani lokaci. Haka dai muka yi ta fama har zuwa lokacin da aka kawo karshen yakin cacar baka."

Rikicin Ruwanda ya shafi aikin a tashar

A shekarar 1990 rikicin kabilanci ya barke a kasar Ruwanda tsakanin kabilun Hutu da Tutsi. A saboda dalilai na tsaro bayan da rikicin ya yi muni, an gina wata katanga da ta kewaye harabar ginin tashar a Kigali. A ranar da aka kammala ginin katangar ce aka fara kuma kisan kare dangi a Ruwanda, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu 800 a cikin wata daya. Injiniya Walter Berger ya tuna halin da suka shiga ciki.

"Abin da ba mu sani ba a wannan rana shi ne kisan kare dangin da aka fara a Ruwanda. Amma washegari mun shaidar cewa wani mummunan abu na faruwa. Nan-take tsoro ya fara shiga zukatan mutane. Sannan mun ga cewa ba za mu iya fita daga harabar tashar ba."

Dakarun gwamnati na 'yan tawaye sun gwabza fada a kusa da harabar tashar, sannan an toshe hanyar da ta hada tashar da tsakiyar birnin Kigali. Sannan 'yan gudun hijira suka yi ta tsallaka katangar tashar don kai wa tudun mun tsira. Su kuwa ma'aikata a tashar sun kasance tamkar firsina a cikin harabar.

Ceto a sa'a ta karshe

A ranar 13 ga watan Afrilu sojojin kundunbala kasar Beljiyem sun yi sa'ar shiga tashar inda suka ceto Jamusawa ma'aikata 11 da iyalansu. Amma aka bar ma'aikata 'yan Ruwanda, ciki har da Rosette Berger wadda 'yar Ruwanda ce da ke auren Bajamushe injiniya Walter Berger.

"Idan ka tsinci kanka a irin wannan hali, fatanka shi ne ka samu mai ceto ko ta wane hali. A lokacin Jamusawa sun kasa kwashe mu. Da farko na yi bakin cikin wannan abu. Amma daga baya na sadaukar da komai na ba wa Allah. In da na bar wurin to da watakila ban kai filin jirgin sama da rai na ba."

An dai soki lamirin dakaraktan tashar Hans Josef Berghäuser da rashin yin wani katabuns na ba wa 'yan gudun hijira kariya daga sojojin Ruwanda. A cikin watan Agusta Walter Berger da abokan aikinsa sun koma Ruwanda inda suka tarar da kasusuwan mutane cikin tashar.

Relaisstation Kigali

Shekaru 50 daga tsaunukan Kigali zuwa duniya baki daya

Ma'aikatan dai sun ci gaba da aiki har zuwa ranar 29 ga watan Maris na wannan shekara ranar da aka rufe tashar bayan da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Ruwanda da Deutsche Welle ta kare ba a kuma sabunta ta ba. Amma ga masu sauraron tashar DW ba wani abin da ya sauya domin za su cigaba da sauraron shirye-shiryen tashar a kan mitocin da aka saba.