Yuyuwar barkewar rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
October 27, 2018Talla
Jagoran tsofuwar kungiyar ta Seleka ne dai Abdoulaye Hissene, ya sanar da hakan a ranar Asabar, kwana daya bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka sauke shugban majalisar dokokin kasar Karim Meckassoua wanda Musulmi ne daga mazabar gunduma ta uku ta Bangui babban birnin kasar. Da yammacin ranar Juma'a ne dai 'yan majalisar suka sauke shugaban nasu, amma kuma a cewar Abdoulaye Hissene na kungiyar ta Seleka, sauke Meckassoua ba a yi shi a kan ka'ida ba, kuma an yi shi ne domin matsayinsa na Musulmi.
A baya dai an kalli zaben shugaban majalisar Karim Meckassoua a matasyin wani mataki na sulhu tsakanin 'yan kasar, ganin cewa shugaban kasar Faustin-Archange Touadéra na a matsayin Kirista.