Bangui: An halaka wasu dakarun MINUSCA | Labarai | DW | 05.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangui: An halaka wasu dakarun MINUSCA

Wasu 'yan bindiga sun hallaka jami'an wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan da suka afkawa jerin gwanon motocinsu a kudancin kasar.


Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na ecwar wasu 'yan bindiga sun hallaka wasu jami'an wanzar da zaman lafiya na na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a kasar lokacin da suka afkawa wasu jerin gwanon motocinsu a kudu maso gabashin kasar.Masu aiko da rahotanni suka ce jami'an wanda 'yan kasar Morroco ne na kan hanyarsu ta yin rakiya ga wasu manyan motoci da ke dauke da man mota, lamarin da ya sanya kwamitin sulhu na MDD din yin Allah wadai da wannan hari.

Tuni dai aka gargadi hukumomin Bangui da su dau matakai na magance masu afkawa jami'an wanzar da zaman lafiya da ke aiki a sassan kasar daban-daban. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta shafe tsawon lokaci ta na fama da tashin hankali da ke da nasaba da siyasa da kuma addini musamman ma dai tsakanin mayakan Seleka da 'yan Antibalaka.