1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalaman batanci ga Annabi ya haifar da rikici

Ramatu Garba Baba
October 20, 2019

Wani rikici da ya barke bayan wallafa kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) yayi sanadiyar mutuwar mutum 4 a yankin Kudancin kasar Bangladesh.

https://p.dw.com/p/3RbFa
Bangladesch Blasphemie Gesetz Ausschreitungen Dhaka
Hoto: Reuters

Kakakin 'yan sanda yankin Mohaiminul Islama ya ce, biyu sun mutu a yayin zanga-zangar yayin da sauran da aka ruga dasu asibiti suka mutu a gadon asibitin. Jami'an  'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen kwantar da tarzomar bayan da rikicin ya ki cinyewa.

Hargitsin ya soma ne bayan da aka gano yadda wani mabiya addinin Hindu, ya soki Annabin tsiran da 'yarsa Nana Fatima a rubutun da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar da ta gabata. Koda 'yan sanda suka kama wanda ake zargin, ya musanta zargin inda ya ce, kutse aka yi wa shafin nasa.