Bangarori daban daban na daukar matakan warware rikicin Mali | Siyasa | DW | 20.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bangarori daban daban na daukar matakan warware rikicin Mali

A yayin da hukumomin Mali ke nuna alamun amincewa da tattaunawa tare da 'yan tawayen da ke da iko da arewacin kasar, da dama daga cikin al'ummar kasar na bayyana bukatar kwato yankin - ko da ta hanyar yaki ne.

Wasu daga cikin 'yan Malin na samun horo a wani sansanin da ke garin Sevare a yankin tsakiyar kasar, kuma duk da cewar ba su da wadatattun kayayyakin da za su saukaka musu samun horon, kamar manyan takalma, amma daukacin matasa 50 da ke samun horon, na cike da fatan taka rawa wajen kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan aware. Daga cikin wadannan matasan kuwa harda Roukiatao Coulibaly:

Ta ce " Ina nanne da zimmar ganin an sake kwato yankin arewacin Mali. Wannan yana da muhimmanci domin kuwa kasar mu ce, kuma akwai bukatar samar da sauyi ga halin da ake ciki. Ba za'a taba rabe Mali ba. Tilas ne kasar ta zama dunkulalliya, kuma saboda haka ne muke anan domin sake 'yanto kasarmu."

Matakin soji ne zai kawo karshen rikicin Mali

Wannan matashiya - 'yan shekara 24 da haihuwa, wadda ke da 'ya'ya biyu dai, na daga cikin kungiyoyin mayaka daban daban da ke garuruwan Mopti da Sevare, wadanda ke fafutukar ganin an kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawayen da ke da tsananin kishin addini da kuma wadanda ke neman ballewa daga kasar. A cewar Moussa Traore, daya daga cikin masu bayar da horon, ya zuwa yanzu kimanin mutane dubu daya ne suka fara samun horo cikin watanni taran da suka gabata, wadanda kuma suke kan hanyar yaye su domin tinkarar 'yan tawayen:

Ya ce " Mun fara basu horon yanda za su sarrafa makamai, domin kuwa muna hada gwiwa da sojoji. Alal misali, idan ina bukatar bindigogi 30 ne, sai in mika bukatar garesu. Abin nufi dai shi ne muna da kyakkyawar alaka da sojojin, domin muna yin aiki tare da su."

Akwai mutane da dama da ke da ra'ayin cewar shiga tsakani - ta hanyar soji ne kawai zai 'yantar da yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawayen kungiyar Ansar Dine da ke da tsananin kishin addini da kuma mayakan kungiyar Aqmi dake zama reshen kungiyar AlQa'ida a yankin Maghrib, sai kuma mayakan Mujao a yankin yammacin Afirka.

Bildbeschreibung: Malische Flüchtlinge in Burkina Faso Schlagworte:Mali, Flüchtlinge, UNHCR, Burkina Faso Überschrift: Malische Flüchtlinge in Burkina Faso Fotograf: Peter Hille Ort: Sag-Nioniogo, Burkina Faso Thematischer Zusammenhang: Malische Flüchtlinge im UNHCR-Flüchtlingslager in Sag-Nioniogo, Burkina Faso

'yan gudun hijirar Mali a Burkina Faso

'Yan gudun hijira na kokawa game da halin da suke ciki a Mali

A Bamako, babban birnin kasar Mali, jama'a da dama na yin Allah wadai ne da mayakan MNLA da ke fafutukar 'yantar da yankin Azawad, wadanda sakamakon kwace ikon da suka yi ne ya tilstawa mazauna yankin tserewa zuwa yankunan kasar da ma wasu kasashen ketare a matsayin 'yan gudun hijira, kuma a yanzu suke kokawa game da halin da suka tsinci kansu a ciki, kamar yanda Azima Mohammed, da aka fi sani da Ali - dan shekara bakwai ke bayyana takaicinsa dangane da yadda al'umomin kasa da kasa suka yi watsi da halin da ake ciki a Mali:

Ya ce " Aqmi matsala ce ga duniya baki daya ba wai ga Mali ko kuma Afirka kadai ba. Matsalar tana shafarmu baki daya. Yanzu lokaci yayi daya kamata tarayyar Turai da Afirka su tallafawa Mali shawo kan matsalar."

Sai dai kuma samun tallafin ketare domin warware rikicin Mali na ja da baya, musamman bayan da a makon jiya, Kaftin Amadou Sanago, tsohon jagorar mulkin sojin kasar daya kifar da gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure, ya sake jagorantar korar firayiministan kasar, ko da shike kuma cikin dan karamin lokaci Diango Cissoko ya maye gurbinsa, amma kuma masu nazarin al'mura na cewar sha'anin siyasa a Mali na cikin rudani.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 20.12.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/176GM
 • Kwanan wata 20.12.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/176GM