Bangaladash ta rataye wasu ′yan adawa biyu | Labarai | DW | 22.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangaladash ta rataye wasu 'yan adawa biyu

Bayan da shugaban Bangaladash ya yi watsi da takardar neman afuwa ne aka rataye wasu 'yan siyasa biyu da suka cin zarafi lokacin yaykin neman 'yancin kasar.

Gwamnatin Bangaladash ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa kan wasu tsaffin 'yan adawa biyu da aka samu da laifin aikata ta'asa a yakin da ya baiwa kasar damar samun 'yancin kanta a shekarar 1971. Ministan cikin gidan Bangaladash ne ya bayyana cewar an rataye tsohon dan majalisa Salahuddin Qader Chowdhury na Jam'iyyar BNP da kuma tsohon minista Ali Ahsan Mohammad Mujahid a gidan yari birnin Dacca bayan da shugaban kasa ya yi watsi da takardar afuwa da suka tura masa.

Kotun Bangaladash ta sami su 'yan adawan da laifin taka rawa a yakin da kasar ta gudanar da Pakistan, inda kimanin mutane miliyan uku suka rasa rayukansu. Sai dai 'yan adawan kasar sun danganta wannan hukunci da bita da kullin siyasa. Tuni ma suka yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari a wannan Lahadin don nuna rashin amincewa da aiwatar da hukuncin na kisa.

Sai dai kuma gwamnati ta Bangaladash ta tsaurara matakan tsaro a Dacca babban birnin da ma dai sauran sassa na kasar.