Banbancin da ke tsakanin kasashen duniya | Amsoshin takardunku | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Banbancin da ke tsakanin kasashen duniya

Kasashe masu arziki suna samun bunkasa saboda matakan karfafa tattalin arziki da ake amfani da su yayin da sauran kasashe ke fafutuka

Habakar tattalin arziki ya samo asali daga kididdigar da ake yi na samun kudaden shigar kasa, inda ake gwada karfin tattalin arziki da abubuwan da kasa take yi da kuma irin abubuwa da kasa take iya samar wa al'uma.

Kasashe masu arziki suna samu kudaden shiga mai yawa tare da iya fitar da kayyakin da aka sarrafa, yayin da kasashe masu tasowa suke da koma baya ta wannan fanni. Kuma babban babban banbancin da ke tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da masu tasowa shi ne, wani abu ne dan kasa zai iya samu a shekara, da abun da dan-kasa zai samu na kyautata rayuwarsa. Idan aka duba wadannan abubuwa kasashe masu arziki sun yi zarra.