Ban kwana da Paparoma Benedikt na 16 | Labarai | DW | 27.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban kwana da Paparoma Benedikt na 16

Mabiya darikar katolika kusan dubu 150 ne suka yi tururuwa a dandain St. Peters da ke birnin Roma don yin ban kwana da Paparoma Benedickt na 16

A cikin jawabin da ya yi ga dimbin jama'a, shugaban na Katolika dan asalin kasar Jamus ya bayyana muhimmacin da ke tattare da murabus dinsa dake zama wanda ba na saban ba. Shi dai Benedict na 16 shine shugaban Katolika na farko da ya yi murabus bisa radin kansa cikin kusan shekaru 600 da suka gabata. Ya tsai da wannan shawara ne yana mai kafa dalili da rashin karfin jiki da kuma samar da ci gaban cocin. Shugaban na Katolika mai shekaru 85, wanda da yammacin wannan Alhamis (28.02.13) ne zai sauka daga wannan mukami ya mika gidiyarsa ga mabiya darikar Katolika da kuma ma'aikatansa game da amincewa da suka yi da murabus dinsa da ya sanar a ranar 11 ga wannan wata na Fabarairu. Paparoma ya nuna gamsuwarsa da irin goyon bayan da ya samu daga mutane da suka hallara suna daga tutoci domin nuna masa kauna.

A watan Maris mai kamawa ne kuma shugabannin coci za su zabi wanda zai gaje shi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita : Saleh Umar Saleh