Ban Ki Moon ya kai ziyarar ba zata a birnin Bangui | Labarai | DW | 05.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki Moon ya kai ziyarar ba zata a birnin Bangui

A matakin nuna aniyar Majalisar Dinkin Duniya game da maido da zaman lafiya da bin doka da oda a Afirka ta Tsakiya, Ban ya gana da mahukuntan kasar.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya kai wata ziyarar ba zata a birnin Bangui, na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wannan Asabar, a wani mataki na nuna aniyar ta Majalisar ta Dinkin Duniya, kan batun tura dakarunta domin su maido da doka da oda a wannan kasa da a kullu yaumin ke cikin rikici na kashe-kashe.

Ban dai yana kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Kigali na kasar Ruwanda, inda zai halarci bukukuwan cika shekaru 20 da kisan kiyashin da aka yi a wannan kasa. Ban Ki Moon ya yada zongo ne a birnin na Bangui inda kuma yake tattaunawa da shugabar rikon kwarya Catherine Samba-Panza.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya na cike da fargaba ta ganin an sake samun wani kisan kiyashin shigen na Ruwanda a wannan kasa inda zai yi bayani a gaban majalisar rikon kwarya domin sake kira ga kasashen duniya da sukai dauki ga Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal