Bam ya halaka gwammai a Afghanistan
June 22, 2017Talla
Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa mutane 34 sun rasa rayukansu a wani bam da mayakan kungiyar Taliban suka tayar a banki a yayin da taron al'umma ke kokarin ciran albashi daga na'urar cirar kudi ta ATM.
Harin wanda ya auku a wannan Alhamis, an kai shi ne a yankin Lashkar Gah da ke daf da birnin Kabul, bayanai sun ce akwai wasu fiye da 50 da suka sami raunuka da aka riga aka ruga da su asibiti. Harin dai ya kasance mafi muni da aka kai kan ayarin jama'a cikin wannan watan na Ramadana. Galibin mutane da suka mutu dai fararen hula ne.