Bala′in fari a Somaliya | Labarai | DW | 08.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bala'in fari a Somaliya

Sama da yara 58000 ke cikin hatsarin mutuwa sakamakon yunwa a kasar Somaliya domin baya ga yakin da kasar ke fama da shi akwai kuma matsalar karancin damina

A wani rahoton da MDD ta fitar yau Litinin 08.02.2016, tace sakamakon tsananin fari da aka yi, a yanzu kasar da yaki ya dai-daita, akwai wani bala'i da ke fisaknatarsu. A cewar rahoto tsananin rashin abinci mai gina jiki musamman ga yara kanana, a yanzu ya kai wani mizani na tada hankali. Inda yanzu yara sama da dubu 30 ke fama da bakar yunwa. Bisa kiyasin MDD, Somaliyawa miliyan hudu da dari bakwai, wato kashi arba'in na al'ummar kasar suna matukar bukatar tallafin abinci.